Wahala a Najeriya: Bankin Duniya Ya Yabi Tinubu, Ya Ba Shugaban Kasa Shawara
- Bankin Duniya ya bayyana goyon bayansa ga manufofin farfado da tattalin arziki da gwamnatin Bola Tinubu ke yi a kasar nan
- Mataimakin shugaban bankin, Indermit Gill ya ce tabbas yan kasar na cikin mawuyacin hali, kuma akwai bukatar a dauki mataki
- Indermit Gill ya shawarci gwamnati kan ta rika raba arzikin da kasar nan ke samu a bangaren fetur da talakawa domin su samu sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Bankin Duniya ya shawarci gwamnatin kasar nan kan dabarun da za ta bi wajen raba arzikin man fetur domin rage talauci.
Mataimakin shugaban bankin, Indermit Gill ya bayyana cewa yan Najeriya na cikin kangin wahala ne saboda rashin aikin yi, rashin ilimi mai inganci da rashin kula a bangaren lafiya.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Mista Indermit Gill ya kara da cewa matasa da yara sun fi kowa shan wahalar da hauhawan farashi ke jawo wa a kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bankin Duniya ya shawarci gwamnatin Tinubu
Jaridar The Cable ta wallafa cewa mataimakin shugaban Bankin Duniya, Indermit Gill na ganin kamata ya yi gwamnati ta rika raba dukiyar da ake samu daga arzikin fetur da talakawa.
Mista Indermit Gill ya kara da cewa bai dace a tattare arzikin ga iya masu kudin kasar ba, domin talakawa na cikin mawuyacin hali saboda wahalar rayuwa.
Bankin Duniya ya goyi bayan manufofin Tinubu
Bankin Duniya na ganin manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasa da ya durkushe.
Bankin, wanda ya rantawa Najeriya biliyoyin Daloli na ganin sai an cigaba da amfani da manufofin na tsawon shekaru 10 zuwa 15 domin gyara tattalin arziki.
Shugaba Tinubu ya kare manufofinsa
A baya kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kare manufofinsa, ya ce ana bukatarsu idan har za a farfado da tattalin arzikin kasa duk da cewa yan Najeriya na kuka.
Shugaban, wanda ya yi magana ta bakin Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, ya ce duk da ana ganin manufofinsa sun rikita kasa, amma a nan gaba yan Najeriya za su ci moriyar matakan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng