"Mun Sani": Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Sa Matakansa ke Kuntatawa Al'umma, Ya Yi Albishir

"Mun Sani": Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Sa Matakansa ke Kuntatawa Al'umma, Ya Yi Albishir

  • Gwamnatin Tarayya ta fadi dalilin da ya sa matakan da ake dauka a bangaren tattalin arziki suka kasance masu tsauri
  • Shugaba Bola Tinubu ya ce babu yadda aka iya dole sai an ɗauki matakan ne domin tsamo kasar daga halin da take ciki
  • Shugaban ya bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki da ma'aikatu masu zaman kansu domin inganta tattalin arzikin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake yin magana kan halin kunci da ake ciki a Najeriya.

Tinubu ya ce duk halin da ake ciki suna sane kuma babu wasu hanyoyin kaucewa hakan saboda ya zama dole.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake magana kan tallafin mai, ya yi albishirin samun sauki

Tinubu ya sake magana kan halin kunci da ake ciki
Bola Tinubu ya bayyana musabbabin wahalar da ake sha a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya fadi silar shiga halin kunci

Shugaban ya bayyana haka yayin wani taro da mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya bayyana cewa dalilin shiga halin kunci da ake ciki bai rasa nasaba da matakan da aka dauka a ƙasar.

Shugaban ya bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki da kamfanoni masu zaman kansu domin kawo sauyi a ƙasa.

Hakan na zuwa ne bayan halin kunci da yan kasar suka shiga dalilin matakan tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta dauka.

Tinubu ya damu da halin da ake ciki

"Wasu daga cikin matakan da muka dauka sun jawo kunci ga al'umma amma kuma hakan ya zama dole ne babu yadda aka iya."
"Zuciyarmu na tare da yan kasa, mun san halin da talakawa da matasa suke ciki a yanzu amma babu yadda zamu yi ne."

Kara karanta wannan

"Wahala a Najeriya:" Bankin Duniya ya yabi Tinubu, ya ba Shugaban kasa shawara

"Tabbas matakan ba su da dadi ko kadan amma ita gaskiya daya ce wanda mafi yawa ba su son jinta."

- Bola Ahmed Tinubu

Tinubu ya ce suna kokarin kammala manyan ayyuka kamar hanyoyi da hanyar jirgin kasa da sauransu domin inganta tattalin arziki.

An kare Tinubu kan zuwa Faransa

Kun ji cewa 'yan Najeriya da dama musamman 'yan adawa sun fara ce ce ku ce yayin da Bola Tinubu ya tafi Faransa daga Birtaniya.

Sai dai fadar shugaban kasa ta fito ta kare tafiye tafiyen shugaban, inda ta ce yana da ikon zuwa duk inda ya ga dama a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.