Yan Fashi Sun Mamaye Unguwa Tsakar Dare, Sun bi Gida Gida Suna Ta’addanci
- Wasu yan fashi da makami sun mamaye wata unguwa cikin dare inda suka rika bi gida gida suna yi wa al'umma ta'addanci
- Mutanen unguwar sun ce yan fashin yi gayya, kuma sun yi harbe harbe, ba su tsaya nan ba, sun sace dukiya mai dimbin yawa
- Bayan wayewar gari, an tafi da mutanen da yan fashin suka yi wa harbi da sara da adduna zuwa asibiti domin jinya da karɓar magani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Akwa Ibom - Al'umma sun kwana cikin tashin hankali a unguwar Ifa Atai Etoi na birnin Uyo a jihar Akwa Ibom.
Yan fashi da makami ne suka yi mamaya a unguwar cikin dare su na bi gida bayan gida su na sata da harbe harbe.

Asali: Original
Jaridar the Nation ta wallafa cewa yan fashi da makamin sun bar mutanen unguwar da mummunar asara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan fashi sun mamaye unguwa a Uyo
A daren Litinin ne miyagu yan fashi da makami suka rika bi gida gida suna sata da harbin mutane a wata unguwa a jihar Akwa Ibom.
Wasu mazauna unguwar sun bayyanawa cewa miyagun shigo gidansu da misalin karfe 1:30 na dare wasu kuma da misalin karfe 2:00 na dare.
Yan fashi sun yi ta'adi a unguwa
Wani da abin ya shafa ya ce mutane sun kai 15 suka shiga gidansa kuma sun fara da harbin matarsa a kafa, suka ce idan ya yi motsi za su harbe shi.
Yan fashin sun yi sara da adda a kayin wani mai gadi mai suna Victor wanda yanzu haka yana asibiti domin karɓar magani.

Kara karanta wannan
'Akwai matsala': Yadda malami 1 ke koyar da daruruwan dalibai a makarantun gwamnati
Kayan da yan fashi suka sace a Uyo
Rahotanni sun nuna cewa yan fashi da makamin sun sace wayoyin hannu da dama, na'ura mai ƙwaƙwalwa, miliyoyin kudi da sauransu.
A yanzu haka dai an sanar da rundunar yan sanda saboda gudanar da bincike ko za a gano miyagun da suka yi ta'asar.
An kona caji ofis a jihar Edo
A wani rahoton, kun ji cewa an samu barkewar mummunar rikici kan zargin garkuwa da mutane da wasu matasa suka yi a jihar Edo.
Rahotanni sun nuna cewa wasu matasa ne da suke zargin ana garkuwa da yan uwansu suka tunkari ofishin yan sanda, suka kona shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng