Shugaban NNPCL Ya Bayyana Ribar da Ake Samu daga Fasa Kwaurin Man Fetur
- Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) Mele Kyari ya yi ƙarin haske kan ribar da ake samu daga fasa ƙwauri
- Mele Kyari ya ce masu fasa ƙwaurin man fetur sun yi amfani da tallafi mai da ake biya wajen samun riba mai yawan gaske
- Ya ƙara da cewa cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi ya sanya an daina samun ƙazamar riba daga fasa ƙwaurin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban kamfanin mai na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya ce masu fasa ƙwaurin man fetur sun yi amfani da tallafin da gwamnati ta riƙa biya wajen samu riba.
Mele Kyari ya bayyana cewa sakamakon biyan tallafin, masu fasa ƙwaurin na samun ribar kusan N17m kan kowace babbar mota da aka kai zuwa ƙasashe makwabta.
Shugaban NNPCL ya magantu kan fasa ƙwaurin fetur
Mele Kyari ya bayyana hakan ne lokacin da da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kamfanin na NNPCL, ya ce fasa-kwaurin da ake yi a kan iyakokin ƙasar nan ya yi ƙamari ne sakamakon biyan tallafin man fetur.
Kyari ya ce masu fasa ƙwaurin na samun ribar N17m a kan duk sawu ɗaya da babbar mota mai dakon lita 6,000 ta yi, rahoton Nairametrics ya tabbatar.
Mele Kyari ya faɗi ribar fasa ƙwaurin mai
Shugaban na NNPCL ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da aka yi ya sanya an daina samun riba daga fasa ƙwaurin.
"A mota mai dakon lita 6,000 ana samun ribar N17m. Ta ya ya za a iya dakatar da waɗannan mutanen waɗanda a sawu biyu kawai za su samu kuɗin da suka wuce darajar motar."
"Amma idan ka kai mota mu ɗauka ta N8m zuwa Maiduguri, duka abin da za ka samu bai wuce N500,000 ba. Me zai sa ina ganin N17m sannan na tafi Maiduguri, na ajiye a gidan mai na tsawon wata ɗaya sannan na samu N3m ko N4m."
- Mele Kyari
IPMAN ta zargi kamfanin NNPCL
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙungiyar dillalan man fetur (IPMAN) na kasa ya zargi kamfanin mai na NNPCL da yi masu shigo-shigo ba zurfi kan farashin fetur.
Alhaji Abubakar Garima ya bayyana cewa NNPCL ya fara sayar masu da kowace litar fetur da tsada daga wuraren dakon fetur din kamfanin a jihar Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng