Gwamnati za Ta Karo Kayan Aiki domin Ragargaje Yan Ta'adda a Arewa

Gwamnati za Ta Karo Kayan Aiki domin Ragargaje Yan Ta'adda a Arewa

  • Gwamnatin tarayya ta kara jaddada matsayarta a kan yaki da ta'addanci da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a Arewa
  • Karamin Ministan tsaro Bello Matawalle da ya ziyarci Sakkwato ya ce za a kara manyan kayan aiki da za su taimaki jami'an tsaro
  • Ya bayyana yadda dakarun rundunar sojin saman kasar nan ke bayar da taimako wajen dakile barazanar tsaro a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Gwamnatin tarayya ta kara tabbatar da cewa za ta fatattaki yan ta'adda da su ka hana jama'a zaman lafiya, musamman a Arewacin kasar nan.

Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ne ya bayyana haka bayan ya ziyarci sabon wurin zaman sojojin saman kasar nan da ake samarwa a Sakkwato.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya fadi abin da zai faru ga masu ba yan ta'adda bayanai

Tsaro
Gwamnati ta yi alkawarin kakkabe rashin tsaro a Arewa maso Gabas Hoto: @FMINONigeria
Asali: Twitter

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da ma'aikatar yada labarai da wayar da kan jama'a ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista, gwamna sun duba aikin tsaro

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu sun kai ziyarar gani da ido kan aikin samar da matsuguni ga sojojin saman kasar nan.

Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya ba su tabbacin samar da karin kayan aiki domin ba sojojin damar cigaba da ragargazar yan ta'adda.

Gwamnati ta yabi sojojin sama kan tsaro

Gwamnatin tarayya ta yaba da namijin kokarin da jami'an rundunar sojin saman kasar nan ke yi wajen fatattakar yan ta'adda da sauran bata-gari a Arewacin kasar.

“ Rundunar sojin sama na cigaba da taka muhimmiyar rawa wajen tsaron kasar nan.

Kara karanta wannan

Boko haram: Sanata Ndume ya fadi gaskiya kan kai masa hari

"Gwamnatin tarayya za ta bayar da dukkanin abubuwan da ake bukata na aiki domin yakar barazanar tsaro a yankin Arewa maso Gabas,"

- Dr. Bello Matawalle.

Yan ta'adda sun ragargaji kawunansu

A baya mun ruwaito cewa rigima ta kaure tsakanin dabar yan ta'adda a jihar Zamfara, inda tsagi guda ya yi nasarar kashe kasurgurmin jagoran yan ta'adda, Kacalla Ibrahim Gurgun Daji.

Kisan Kachalla wani gagarumin al'amari ne da zai taka rawa wajen dakile ayyukan yan ta'adda, musamman wandanda su ka hana jama'a kwanciyar hankali a Zamfara da kewaye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.