An Shiga Tashin Hankali da Wani Gini Mai Hawa 2 Ya Rufta, Bidiyo Ya Bayyana
- Mutane sun yi takansu yayin da wani bene mai hawa biyu ya rufta da safiyar ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024 a Legas
- Rahotanni sun nuna cewa dukkan mutanen da ke zaune a benen sun yi takansu gabanin faruwar mummunan lamarin a yau
- A rahoton farko da ta tattara, hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas ta ce babu wanda ya rasa ransa a rugujewar ginin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Wani gini mai hawa biyu ya ruguje a kan layin Amusu da ke unguwar Orile Iganmu a jihar Legas da sanyin safiyar yau Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024.
Wani faifan bidiyo mai ta da hankali da ake yaɗawa a soshiyal midiya ya nuna yadda ginin ya rufta ba zato ba tsammani.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa mutanen da ke wurin sun yi rige-rigen guduwa domin neman tsira a lokacin da suka fahimci ginin na shirin ruftawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ginin ya ruguje a Legas
Bidiyon da aka naɗa ya nuna lokacin da mutane suka fara tsere domin neman mafaka bayan ginin ya fara ƙarar rugujewa.
A rahoton masaniyar farko da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas watau LASEMA ta fitar, ta ce babu wanda ya mutu sakamakon rushewar ginin.
Jami'in hulɗa da jama'a na LASEMA, Nosa Okunbor ya ce dukkan mutanen da ke cikin ginin sun fita salin-alin gabannin ya kai ga ruahewa.
Jami'an LASEMA sun kai ɗauki
Ya ce tuni tawagar ba da agaji da ceto suka isa wurin domin fara lalube ko wani ya maƙale a ɓaraguzan ginin, rahoton Daily Trust.
Okunbor ya ce:
"Jami'anmu da tawagar ƴan kwana-kwana da rundunar ƴan sanda sun kai ɗauki wurin domin jawo hankalin mutane su tashi daga kewayen ginin da ya rufta don kaucewa wata matsalar."
Gobara ta babbake gidajen ma'aikata a Legas
Rahotanni sun bayyana cewa gobara ta babbake rukunin gidajen ma'aikatan gwamnatin jihar Legas da ke Odunsanmi a Ogba.
An tattaro cewa gobarar ta babbake wani gida mai hawa har uku da wani gida mai dakuna biyu da sauran wasu gidajen a Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng