"Mu ma Mu na Jin Jiki:" Ministan Tinubu Ya Ce Gwamnati Na Shirin Magance Matsi

"Mu ma Mu na Jin Jiki:" Ministan Tinubu Ya Ce Gwamnati Na Shirin Magance Matsi

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta na sane da irin wahalar hauhawar farashi da matsin rayuwa da yan kasar nan ke ciki
  • Karamin Ministan tama da karafa, Uba Maigari ne ya fadi haka, ya ce jama'a ba sa ganin kokarin gwamnati saboda rashin bibiya
  • Ya ce amma idan aka duba da kyau, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na daukar wasu muhimman matakai kan maye gurbin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Karamin Ministan tama da karafa, Uba Maigari ya bayyana irin kokarin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke yi na magance matsalolin kasar nan.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Uba Maigari ya bayyana cewa daga cikin matakan da aka samar yanzu akwai bunkasa amfani da ababen hawa masu amfani da gas din CNG.

Minisya
Minista tama da karafa, Uba Maigari ya ce ana kokarin magance matsalar rayuwa Hoto: Tajuddeen Nuhu
Asali: Facebook

A hira da ya yi da Channels Televsion, karamin Ministan na ganin mutane ba sa ganin wasu daga cikin kokarin gwamnati ne saboda ba sa dubawa da kyau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Tinubu ya ce su na shan wahala

Karamin Ministan tama da karafa, Uba Maigari ya ce su na jin duk wata wahala da yan kasar nan ke ji saboda su ma yan kasa ne.

Ya ce gwamnatin tarayya da mukarrabanta su na sane da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki, kuma ana kokarin magance matsalolin.

Minista ya fadi dalilin rashin ganin kokarin Tinubu

Gwamnatin tarayya ta ce jama'ar kasar nan ba su ganin irin matakan da ta ke dauka wajen shawo kan wahalar rayuwa da ake ciki saboda ba su bibiyar ayyukanta yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

Karamin Ministan tama da karafa, Uba Maigari ya ce ko ababen hawa da aka gani a fadar gwamnati ta Aso Rock, kadan ne daga wadanda za a raba ga yan kasar nan.

Ya kara da cewa yanzu haka akwai kwamitin da ke aiki wajen ganin an samar da gas din CNG da wuraren samunsa da ma mayar da ababen hawa a kasar nan masu amfani da iskar gas din.

Matar Tinubu ta ce mijinta na kokari

A wani labarin kun ji cewa mai dakin shugaban kasa, Sanata Oluremi Bola Tinubu ta bayyana cewa mijinta ba shi da hannu a cikin wahalar da yan kasar nan su ke sha na hauhawar farashi.

Sanata Oluremi Tinubu ta ba wa mijinta, Bola Ahmed Tinubu kariya duk da matsalar hauhawar farashin fetur da tabarbarewar tattalin arziki da ake zargin manufofin gwamnati sun jawo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.