‘Babu Dawowa Bariki sai an Gama da Yan Bindiga Baki Daya,’ An yi wa Sojojin Najeriya Caji

‘Babu Dawowa Bariki sai an Gama da Yan Bindiga Baki Daya,’ An yi wa Sojojin Najeriya Caji

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi kira na musamman ga sojoji kan tunkarar yan bindiga da sauran miyagu masu tayar da fitina a kasar nan
  • Manjo Janar Kelvin Aligbe ne ya sake yi wa sojojin caji a wani taron jarrabawar karin matsayi da aka yi wa sojojin Najeriya a Ondo
  • Rundunar sojin ta yi kiran ne bisa ganin yadda suka fara samun nasara kan yan bindiga a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Sojojin Najeriya sun kara daukan haramar kawo karshen yan ta'adda a dukkan sassan kasar nan.

An buƙaci sojojin ƙasar nan da su cigaba da sakin wuta kan yan bindiga a dukkan sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Allah bai halicci dan Najeriya domin shan wahala ba,' Obasanjo ya dura kan shugabanni

Sojojin Najeriya
An yi wa sojoji caji kan kawar da yan bindiga. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Manjo Janar Kelvin Aligbe ne ya yi wa sojojin umarni a jihar Ondo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin gamawa da yan bindiga a Najeriya

Manjo Janar Kelvin Aligbe ya bukaci sojojin Najeriya su tabbatar da gamawa da yan bindiga kafin shirin komawa bariki.

Babban sojan ya tabbatar da cewa dole su kammala da yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk wata barazanar tsaro kafin a dawo bariki a fuskanci wasu matsalolin ƙasar.

Dole sojoji su samar da zaman lafiya a duniya

Manjo Janar Kelvin Aligbe ya kara yi wa sojojin Najeriya cewa dole su zauna cikin shirin samar da tsari a ko da yaushe.

Ya tabbatarwa sojojin cewa samar da zaman lafiya a yankunan Najeriya da ma duniya baki daya ba abin da za a yi wasa da shi ba ne.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi lokacin fita a kangi, ya kawo hanyoyin magance matsaloli

Sojoji za su cigaba karbar horo

Manjo Janar Kelvin Aligbe ya yi kira ga sojojin da su cigaba da mayar da hankali kan horon karin matsayi da ake musu a jihar Ondo.

The Nation ta wallafa cewa ya ce horon zai taimaka wajen ba su dabarun da za su iya yakar yan ta'adda musamman yanzu da suka dauko karya lagon miyagu a Najeriya.

An kashe babban dan bindiga a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojoji ta samu gagarumar nasara kan yan ta'adda da sauran miyagu a jihohi daban daban cikin mako daya.

A jihar Jigawa da ke yankin Arewacin Najeriya, sojojin sun yi nasara hallaka jagoran yan ta'adda da ke kira Mai Hijabi yayin wata fafatawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng