Tsadar Fetur: Sauki Ya Kusa Samuwa, Matatar Dangote da Yan Kasuwa za Su Zauna

Tsadar Fetur: Sauki Ya Kusa Samuwa, Matatar Dangote da Yan Kasuwa za Su Zauna

  • An fara shinshino saukin farashi yayin da matatar Dangote ke shirin tattaunawa da yan kasuwa domin cimma matsaya kan dakon fetur
  • Ana sa ran gudanar da tattaunawar a ranakun Talata da Laraba domin jin a kan nawa matatar Dangote zai sayar da fetur ga yan kasuwa
  • Masana na ganin zaman zai kawo wadatar man fetur tare da samun sassaucin tsadar farashinsa sabanin halin da ake ciki a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Masu kasuwancin mai za su zauna da matatar Dangote domin tattauna farashin da matatar za ta sayar masu da fetur.

Kara karanta wannan

Likitoci, lauyoyi sun nemi Tinubu ya warware matakin NNPCL da fetur ya kai N1030

Za a yi zaman ne tsakanin ranakun Talata da Laraba biyo bayan dama da gwamnati ta ba yan kasuwa na dauko fetur kai tsaye daga matatar.

Dangote
Yan kasuwa da matatar za su gana kan farashin litar fetur Hoto: Dangote Industries/NNPC Limited
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa ana sa ran a samu rangwame a farashin litar fetur domin kowane dan kasuwa zai so ya sayar da hajarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin fetur na shirin tattaunawa da Dangote

A makon da ya gabata ne matatar Dangote ta bukaci kungiyar 'Petroleum Retail Outlet Owners Association of Nigeria' ta sake mika bukatarta na fara dakon fetur. A bangarenta, kungiyar dilalan fetur ta IPMAN ta ce fara sayo fetur daga matatar Dangote zai kawo daidaito a farashi da samuwar mai a kasa., kamar yadda Daily Post ta wallafa.

Dangote vs Yan kasuwa: Masana sun hango sauki

Masana a bangaren man fetur irinsu Injiniya Haruna Ubandoman Rogo na ganin kawo karshen kamfanin NNPCL na dakon fetur kai tsaye daga matatar Dangote abu ne mai kyau. Injiniya Ubandoman Rogo ya kara da cewa ana sa ran samun saukin farashi a gidajen mai bayan tattaunawar ta kammala ba tare da an samu cikas ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

IPMAN ta zargi NNPCL da jawo tsadar fetur

A baya mun wallafa cewa kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa kamfanin NNPCL ne ke jawo tsadar farashin man fetur a kasar nan.

Kungiyar IPMAN ta zargi NNPCL da sayar wa yan kasuwa kowace litar fetur a sama da N1,000 duk da ya dauko shi da sauki daga matatar Dangote.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.