'Ku Shirya Zaman Kanku Tun Yanzu', An ba Yan Arewa Shawara kan Shirin Raba Najeriya

'Ku Shirya Zaman Kanku Tun Yanzu', An ba Yan Arewa Shawara kan Shirin Raba Najeriya

  • Farfesa Abubakar Sani Lugga ya yi magana kan kiraye-kirayen da yan Kudu ke yi game da raba Najeriya
  • Farfesan ya shawarci al'ummar yankin Arewa da su hada kai kamar yadda Kudancin kasar ke yi a bangaren tsaro
  • Lugga ya ce dole yan Arewa su shirya zaman kansu musamman da ake hasashen raba Najeriya domin tsayawa da kafafunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Yayin da wasu yankuna ke kiran a raba Najeriya, Farfesa ya ba yan Arewa shawara.

Farfesa Abubakar Sani Lugga ya ce ya kamata yan Arewa su shirya rayuwa bayan raba ƙasar Najeriya.

An shawarci yan Arewa kan shiryawa bayan raba Najeriya
Farfesa Sani Abubakar Lugga ya magantu kan yiwuwar raba Najeriya. Hoto: Muhammad Aminu Kabir.
Asali: Facebook

Farfesa ya ba yan Arewa muhimmiyar shawara

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi lokacin fita a kangi, ya kawo hanyoyin magance matsaloli

Vanguard ta ce Farfesan ya bayyana haka ne yayin taro a jihar Katsina da kungiyar Coalition of Northern Group ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lugga ya ce tun yanzu ya kamata Arewa ta shirya da kuma hada kai domin fuskantar rayuwa bayan rabuwa kamar Kudancin kasar.

Wazirin Katsina na 5 ya ce daukar matakin ya zama dole duba da kiraye-kiraye daga Kudancin kasar da a raba Najeriya.

Farfesa Lugga ya koka game da rashin hadin kai a Arewacin kasar kamar yadda kungiyoyin neman yanci suke a Kudancin Najeriya.

Ya bukaci yan Arewa su hada kai wurin koyon darasi daga yan Kudu musamman da suka dakile matsalar tsaro.

An caccaki shugabanni kan watsi da matsalar tsaro

A bangarensa, shugaban kungiyar, Jamilu Charanchi ya koka kan yadda rashin tsaro ya yi katutu a yankin Arewacin Najeriya.

Charanchi ya nuna damuwa kan yadda shugabannin Najeriya ke nuna fifiko kan zabe fiye da sauran lamuran kasa musamman bangaren tsaro.

Kara karanta wannan

Neman beli: Kotu ta kara hankaɗa keyar jami'in Binance zuwa kurkuku

Dattawan Arewa sun koka kan rashin tsaro

Kun ji cewa Kungiyar ACF ta bayyana fargaba kan yadda rashin tsaro ke karuwa a dukkanin sassan Arewacin Najeriya.

Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu ya ce akwai babbar barazana a yankin da neman tarwatsa ta.

Dalhatu ya nuna takaicin yadda matakan yaki da rashin tsaro ba su dakile matsalar da ake fama da ita a Arewacin kasar musamman ta bangaren tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.