Duk da Halin Kunci, Gwamna Ya Kakaba Biyan Haraji Kullum kan Gawarwaki da Aka Adana

Duk da Halin Kunci, Gwamna Ya Kakaba Biyan Haraji Kullum kan Gawarwaki da Aka Adana

  • Yayin da ake tsaka da shan wahala na tsadar rayuwa, gwamna a Najeriya ya kara kawo sabon biyan haraji a jiharsa
  • Gwamnatin jihar Enugu ta tabbatar da kakaba haraji a dakunan ajiye gawarwakin jihar a kullum domin rage cunkoso
  • Shugaban hukumar tattara kudade, Emmanuel Nnamani ya ce za a ke biyan N40 kullum saboda rage yawan ajiye gawa da ake yi da gan-gan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu - Gwamnatin jihar Enugu ta kakaba sabon haraji da za ake biya kullum a dakunan ajiye gawarwaki.

Gwamnatin jihar ta sanya biyan harajin N40 a kullum domin dakile barin gawa ta dade ba tare da dauke ta ba a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Likitoci, lauyoyi sun nemi Tinubu ya warware matakin NNPCL da fetur ya kai N1030

An kakabawa al'umma biyan haraji kan gawarwakin da aka adana
Gwamnatin jihar Enugu ta sanya biyan haraji kan gawarwakin da aka adana. Hoto: Peter Mbah.
Asali: Facebook

An kakaba haraji kan gawarwaki a Enugu

Shugaban hukumar tattara kudaden shiga a jihar, Emmanuel Nnamani shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nnamani ya ce bayyana haka a jiya Asabar 12 ga watan Oktoban 2024 yayin da yake jawabi ga masu kula da dakunan ajiye gawarwaki.

Sanarwar ta ba masu kula da gawarwakin umarnin a biya N40 a kullum kan gawar da ba a binne ba ciki awanni 24.

Yadda za ake biyan harajin gawa a Enugu

Har ila yau, kudin za a biya kafin ɗaukar gawar wanda zai tafi kai tsaye zuwa asusun jihar a matsayin harajin gawa.

Shugaban hukumar ya ce wannan haraji ba sabon abu ba ne yana cikin dokokin haraji a jihar shekaru da dama, The Guardian ta ruwaito.

Ya kuma ƙaryata jita-jitar da ake yadawa a kafofin sadarwa cewa za ake biyan harajin N4,000 ne a kullum.

Kara karanta wannan

'Ka biya mu daga tushe', Sarakuna a Arewa sun roki Tinubu kan biyansu hakkokinsu

Enugu: An zargi basarake da sace matashi

Mun baku labarin cewa wani basarake a jihar Enugu ya shiga matsala bayan zargin yin garkuwa da matashi saboda filin gado.

Ana zargin Ezineso Oduma, Igwe Daniel Okechukwu Njoku da dauke matashi, Michael Njoku da karbar makudan kudi har N2.5m.

Iyalan matashin sun roki gwamnatin jihar Enugu da hukumar tsaro ta DSS ta hukunta basaraken kan boye Michael da ake zargin ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.