'Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Tafi Faransa,' Gwamnati Ta Yi wa Masu Adawa Martani

'Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Tafi Faransa,' Gwamnati Ta Yi wa Masu Adawa Martani

  • 'Yan Najeriya da dama musamman 'yan adawa sun fara ce ce ku ce yayin da Shugaba Bola Tinubu ya tafi Faransa daga Birtaniya
  • Legit Hausa ta rahoto cewa shugaban kasar ya tafi Birtaniya domin yin hutu makonni biyu, amma daga bisani ya wuce Faransa
  • Sai dai fadar shugaban kasa ta fito ta kare tafiye tafiyen shugaban, inda ta ce yana da ikon zuwa duk inda ya ga dama a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fadar shugaban kasa ta kare tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a kasashen waje bayan ya sanar da cewa zai tafi hutun makonni biyu.

A ranar 2 ga watan Oktoba, fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Shugaba Tinubu zai Abuja zuwa Birtaniya domin hutun makonni biyu a wani bangare na hutun shekara.

Kara karanta wannan

An samu mutumin farko da aka gani da Tinubu a Ingila, ya fadi halin da ake ciki

Fadar shugaban kasa ta yi magana kan dalilin tafiyar Tinubu Faransa daga Birtaniya
Fadar shugaban kasa ta kare Tinubu kan tafiyar da ya yi zuwa Faransa daga Birtaniya. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta rahoto cewa 'yan adawa da wasu 'yan Najeriya sun yi ta ce ce ku ce bayan da aka samu labarin cewa Tinubu zai zarce Faransa daga Birtaniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tafiye tafiyen Tinubu a kwanakin nan

A ranar 29 ga watan Agusta, Tinubu ya bar Abuja zuwa kasar Sin amma ya tsaya a Dubai kafin ya isa birnin Beijing a ranar 1 ga watan Satumba domin ziyarar aiki da taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC).

A ranar 16 ga Satumba, shugaban ya koma Abuja bayan ziyarar da ya yi na tsawon makonni biyu masu amfani a Sin, Dubai da Birtaniya.

A ranar Juma’a, 12 ga Satumba, Kabir Masari, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa ga shugaban kasa, ya ce ya ziyarci Tinubu a gidansa da ke kasar Birtaniya.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Gwamnati ta kare tafiye tafiyen Tinubu

Wannan labari ya haifar da kumfar baki inda wasu 'yan Najeriya ke diga ayar tambaya kan tafiye-tafiyen da shugaban ya yi a kasashen waje.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren Juma’a, Onanuga ya ce a halin yanzu shugaban yana hutun makonni biyu kuma yana iya tafiya duk inda ya ga dama.

“Shugaba Tinubu yana hutun makonni biyu. Ba a taƙaice hutunsa a Birtaniya ba. Wannan rayuwarsa ce. Zai iya zuwa duk inda ya ga dama. Har yanzu yana kan hutunsa."

- A cewar Onanuga.

Tinubu ya zarce Faransa daga Birtaniya

Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi birnin Paris na kasar Faransa yayin da ya ke hutu a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Babban mai taimakawa shugaba Tinubu na musamman kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari ya bayyana cewa Tinubu zai gudanar da ayyuka a Paris din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.