Likitoci, Lauyoyi Sun Nemi Tinubu Ya Warware Matakin NNPCL da Fetur Ya Kai N1030

Likitoci, Lauyoyi Sun Nemi Tinubu Ya Warware Matakin NNPCL da Fetur Ya Kai N1030

  • Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da ta likitocin Kudu-maso-Gabas (FOSAD) sun yi Allah wadai bayan kara kudin man fetur
  • A cikin sanarwa daban daban da kungiyoyin suka fitar, sun bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta janye karin kudin man
  • Kungiyoyin sun yi tarayya a kan cewa karin kudin zai jawo wahalhalu da yawa, lamarin da zai kuma jefa ‘yan kasar cikin talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta bukaci a gaggauta janye karin kudin fetur na baya bayan nan da ya sa litar man ta koma N1,030.

Shugaban kungiyar NBA na kasa, Mazi Afam Osigwe (SAN) ne ya gabatar da wannan bukatar a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Likitoci da lauyoyi sun nemi gwamnatin tarayya ta jenye karin kudin fetur
Lauyoyi da likitoci sun yi Allah wadai bayan NNPCL ya kara kudin fetur. Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

NBA ta nemi a janye karin kudin fetur

Kungiyar ta nuna damuwarta kan yadda gwamnatin ke ci gaba da daukar irin wadannan matakan ba tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki ba, inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazi Afam Osigwe ya ce:

“Saboda haka muna kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin janye wannan karin kuma ta gaggauta aiwatar da matakan da za su dakile illar hauhawar farashin man fetur.
“Matakan za su hada da saka hannun jari a matatun cikin gida, saukaka sufuri, rage haraji ga masu karamin karfi, gyaran hanyoyi, inganta tsaro ta yadda manoma za su yi noma."

Tsadar mai: Likitoci sun yi Allah wadai

Hakazalika, kungiyar likitocin Kudu-maso-Gabas (FOSAD) ta yi Allah-wadai da karin kudin fetur da ta ce yana kara janyo tabarbarewar tattalin arziki, a cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr Stephen Nwala ya sanya wa hannu, FOSAD ta bukaci a janye karin kudin man a mayar da shi tsohon farashinsa.

Dokta Stephen Nwala ya nuna cewa karin kudin man fetur da aka yi ya jawo wahalhalu da yawa, lamarin da ya jefa ‘yan kasar da dama cikin talauci.

"Hakazalika karin kudin fetur din ya haifar da matsala ga ‘yan kasuwa da iyalai a fadin kasar nan, don haka muke kira da a gaggauta janye karin."

- A cewar sanarwar.

"NNPCL ya dawo mana da kudinmu" IPMAN

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan kasuwar mai (IPMAN) sun hurowa kamfanin NNPCL wuta awanni bayan ya kara kudin da yake sayar masu da fetur.

Shugaban kungiyar IPMAN, Abubakar Shettima ya bukaci NNPCL ya mayarwa 'yan kungiyar kudadensu idan ba zai sayar masu da man a tsohon farashi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.