Kashim Shettima Ya Fadi Lokacin Fita a Kangi, Ya Kawo Hanyoyin Magance Matsaloli

Kashim Shettima Ya Fadi Lokacin Fita a Kangi, Ya Kawo Hanyoyin Magance Matsaloli

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana himmatuwar gwamnatin Bola Tinubu wurin inganta rayuwar al'umma
  • Shettima ya nuna damuwa kan halin da kasar ke ciki na rashin ayyukan yi da kuma uwa-uba tsadar rayuwa a yanzu
  • Kashim ya ba da tabbacin cewa nan da yan wasu watanni kadan komai zai daidaita ya dawo yadda ake so a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi magana kan hali kunci da ake ciki a Najeriya.

Kashim ya ce nan da yan wasu watanni kadan masu zuwa komai zai daidaita a Najeriya kamar ba a yi ba.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, hadiminsa ya fadi halin da ya ke ciki

Shettima ya koka kan halin matsin rayuwa da aka ciki
Kashim Shettima ya ba da tabbacin fita a kangin da ake ciki nan ba da jimawa ba. Hoto: Kashim Shettima.
Asali: Facebook

Shettima ya fadi shirin Tinubu a Najeriya

Shettima ya bayyana haka ne a birnin Lafia da ke jihar Nasarawa a jiya Asabar 12 ga watan Oktoban 2024, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan Borno ya ce dole a inganta harkokin kasuwanci da kuma dakile rashin ayyukan yi a kasar.

Ya bayyana himmatuwar gwamnatin Bola Tinubu wurin inganta rayuwar yan Najeriya domin rage musu wahala, Punch ta ruwaito.

Shettima ya nemo hanyar magance matsalolin Najeriya

"Tsarin da aka kawo zai ba yan Najeriya damar yin fice a gida da kuma ƙasashen ketare."
"Ya kamata mu kawo karshen rashin tsari wurin haihuwa da yawan mace-macen mata da kuma yara kasa da shekaru biyar."
"Lokaci ya yi da za mu kawo sauyi a yawan al'umma da muke da su da ba su samun ingantacciyar rayuwa."

Kara karanta wannan

'Ba laifinsa ba ne', Ndume ya fadi nufin Tinubu, ya roki alfarma bayan tsadar fetur

- Kashim Shettima

Wannan na zuwa ne yayin da yan kasa ke cikin mawuyacin hali tsadar rayuwa da ya haddasa yunwa a fadin kasa da har matasa suka fantsama zanga-zanga.

Bikin ranar haihuwa Shettima ya roki al'umma

Kun ji cewa yayin da aka gudanar da bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, Kashim Shettima ya shawarci al'umma.

Mataimakin shugaban kasar ya ce bai kamata abokan arziki da 'yan uwa su kashe kudi domin taya shi murnar ranar ba.

Shettima ya bukace su da su yi amfani da kudin wurin taimakon marasa ƙarfi da kai kudin gidajen marayu da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.