DSS Ta Shiga Tsakani kan Rigimar Kungiyar IPMAN da NNPCL, an Samu Matsaya

DSS Ta Shiga Tsakani kan Rigimar Kungiyar IPMAN da NNPCL, an Samu Matsaya

  • A karshe, hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta shiga tsakani kan rigimar kungiyar IPMAN da kamfanin NNPCL
  • Daraktan hukumar DSS, Adeola Ajayi shi ya bukaci ganawar domin dinke barakar da ke tsakaninsu game da farashin man fetur
  • Daga ƙarshe, an samu mafita a tsakaninsu yayin ganawar da ta samun halartar shugaban NNPCL, Mele Kyari dana IPMAN, Abubakar Maigandi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake rigima tsakanin kamfanin NNPCL da dillalan mai, hukumar DSS ta shiga lamarin.

Shugaban hukumar, Adeola Ajayi shi ya bukaci zama na musamman da bangarorin biyu domin samun mafita.

Hukumar DSS ta yi ganawa da NNPCL da IPMAN kan rigimar da ke tsakaninsu
Hukumar DSS sasanta rikicin kungiyar IPMAN da kamfanin NNPCL. Hoto: NNPC Limited.
Asali: Facebook

An yi ganawa tsakanin IPMAN da NNPCL

Kara karanta wannan

Da gaske alaka ta yi tsami tsakanin Majalisar Tarayya da Tinubu? an samu bayanai

Sakataren yada labaran ƙungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike shi ya tabbatar da haka ga jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ukadike ya ce ganawar ta samu halartar shugaban hukumar NMDPRA da kuma na kamfanin NNPCL, Mele Kyari.

Ya ce musabbabin ganawar akwai matsalar farashi tsakaninsu da matatar Dangote da kuma rashin siyarwa IPMAN kaya.

"Daraktan hukumar DSS ya gayyace mu ganawa ta musamman domin samun matsaya kan rigimar IPMAN da NNPCL."
"Musabbabin ganawar shi ne rashin bin ka'idar siyar da kaya ga IPMAN da kuma matsalar farashi tsakaninmu da NNPCL."
"An samu matsaya a ganawar karkashin jagorancin shugaban IPMAN, Abubakar Maigandi cewa NNPCL ta amince da ba kungiyar damar daukar kaya."

- Chinedu Ukadike

Legit Hausa ta yi magana da wani mai harkokin da hada-hadar mai a Gombe kan rigimar IPMAN da NNPCL.

Jungudo Muh'd Abdullahi ya ce rigimar tana tasiri kan farashin man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

Dillalai sun fadi sakamakon da tattaunawa da matatar Dangote za ta haifar

Jungudo ya ce shiga lamarin da DSS ta yi ana sa ran ya haifar da ɗa mai ido.

Ya kuma koka kan yadda farashin ke shafar harkokin kasuwancinsu inda ya ce sabanin tunanin mutane ba su jin dadin lamarin.

Karanta karin wasu labaran kan NNPCL, IPMAN:

NNPCL ya janye shiga tsakanin Dangote da IPMAN

Kun ji cewa Kamfanin mai na NNPCL ya tsame kansa daga shiga tsakani a harkar kasuwancin man fetur a matatar Aliko Dangote.

Kamfanin ya dauki matakin domin gudun biyan raran kudi yayin da ya ke shiga tsakanin dillalan mai da matatar Dangote.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.