Tuna Baya: Kalaman da Tinubu Ya Jefi Jonathan da Su a 2012 kan Cire Tallafin Mai

Tuna Baya: Kalaman da Tinubu Ya Jefi Jonathan da Su a 2012 kan Cire Tallafin Mai

  • A shekarar 2012, Bola Tinubu ya caccaki shugaban kasa a wancan lokaci, Goodluck Jonathan kan cire tallafin mai
  • Tinubu a lokacin shi ne jagoran tsohuwar jam'iyyar ACN ya soki tsarin tattalin arzikin Jonathan da cewa zai bautar da mutane
  • Sai dai kuma a ranar da Shugaba Bola Tinubu ya dauki rantsuwar kama aiki, ya cire tallafin babu wani bata lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cire tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayun 2023 bayan rantsar da shi.

Tun daga wannan rana abubuwa suka sauya a kasa inda farashin mai ya tashi tare da kayan masarufi.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, hadiminsa ya fadi halin da ya ke ciki

An tuno yadda Tinubu ya soki Jonathan kan cire tallafin mai
Kalaman Bola Tinubu kan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan game da cire tallafi a 2012. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Goodluck Jonathan.
Asali: Twitter

Cire tallafi: Tinubu ya soki Jonathan a 2012

Daily Trust ta ruwaito yadda Tinubu ya caccaki tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan cire tallafin mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A 2012, jagoran jam'iyyar ACN a wancan lokaci, Tinubu ya yi Allah wadai da cire tallafin mai a mulkin Jonathan.

Tinubu ya zargi Jonathan da cin amanar al'umma da yake jagoranci inda ya kira cire tallafin da 'harajin Jonathan '.

Shugaban ya ce ba zai kira Jonathan mugu ba kuma bai yadda ba shi da tausayi ba duba da kunci da ya jefa al'umma, cewar rahoton PM News.

Tinubu ya caccaki tsarin tattalin arzikin Jonathan

"Ba zan ce Jonathan mugu ba ne, amma tsarin tattalin arzikinsa sun kauce hanya kuma akwai mugunta."
"Saboda ana ba shi gurguwar shawara kan inganta tattalin arziki, mutane da yawa za su zama bayi."

Kara karanta wannan

An samu mutumin farko da aka gani da Tinubu a Ingila, ya fadi halin da ake ciki

"Wannan matsala za ta yi ta binsa kuma zai zama shi ne abin da zai kafa tarihi kansa."

- Bola Tinubu

NLC ta ce mulkin Jonathan ya fi na Tinubu

Kun ji cewa kungiyar kwadago ta NLC ta fadi gwamnatoci biyu da suka dara na Shugaba Bola Tinubu a tsarin tattalin arziki.

Kungiyar ta ce gwamnatocin Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari sun yiwa na Tinubu fintinkau kan tsare-tsare masu kyau.

Wannan na zuwa ne bayan wasu matakai da Tinubu ke dauka na tattalin arziki wadanda suka jefa al'umma cikin matsi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.