Gwamna Ya Faranta Ran Ma'aikata, Zai Biya N73,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi
- Gwamnan jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya amince zai biya ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi
- Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana cewa zai biya ma'aikatan jihar N73,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi
- Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamna na APC a zaɓen jihar da ke tafe a watan Nuwamban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Gwamnan Ondo kuma ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba, Lucky Aiyedatiwa, ya amince da biyan sabon mafi ƙarancin albashi.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya amince zai biya ma'aikatan jihar mafi ƙarancin albashi na N73,000.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamna na APC a ƙaramar hukumar Ondo ta Yamma a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Aiyedatiwa zai biya ma'aikata N73,000
Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa, Cif Olayide Adelami da manyan jiga-jigan jam'iyyar APC, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ba da muhimmanci kan jin daɗin ma'aikatan jihar.
"Muna zaburar da ma’aikatanmu ta hanyar kawo shirye-shiryen horarwa daban-daban, kuma ana biyansu albashi a kan lokaci."
"Ba a biyo mu bashi kuma bari na sanar da ku cewa wannan gwamnatin ta yanke shawarar aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi."
"Duk da cewa mafi ƙarancin albashi ya kamata ya zama N70,000, namu zai kasance N73,000. Za mu ci gaba da inganta jin daɗin ku. Zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024, ku fito ku zaɓi APC."
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa
Gwamnan Oyo zai biya albashin N70,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Gwamna Seyi Makinde ya bayyana cewa zai fara biyan mafi ƙarancin albashin da zarar an daidaita batun ƙarin da za a yi a albashin.
Asali: Legit.ng