Za a Kirkiri Jami’ar Tinubu Ta Musamman, an Fadi Yadda Tsarinta Zai Kasance

Za a Kirkiri Jami’ar Tinubu Ta Musamman, an Fadi Yadda Tsarinta Zai Kasance

  • Yayin da Jami'o'i ke cikin mayuwacin hali a Najeriya, Majalisar Dokoki ta gabatar da kudiri domin kirkirar wata Jami'a
  • Mataimakin shugaban Majalisar, Hon. Benjamin Kalu da wasu mambobi guda takwas suka gabatar da kudirin a gabanta
  • Jami'ar ta Bola Tinubu, idan aka kirkire ta za ta ba da karfi wurin inganta harsunan gida Najeriya da kuma al'adun kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Tarayya tana kokarin kirkirar sabuwar Jami'a ta musamman da sunan Bola Tinubu.

Mataimakin shugaban Majalisar Dokoki, Hon. Benjamin Kalu shi ya jagoranci gabatar da kudirin da wasu mambobi takwas.

An fara shirin samar da Jami'ar Tinubu a Najeriya
Ana shirin kirkirar sabuwar Jami'ar Bola Tinubu a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Za a kirkiri sabuwar Jami'ar Tinubu a Najeriya

Kara karanta wannan

Matar shugaba Tinubu ta nuna halin girma, ta yi kyautar kudi N1bn

Punch ta ruwaito za a kirkiri sabuwar Jami'ar ce ta Gwamnatin Tarayya domin bunkasa harsunan gida Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gabatar da kudurin na zuwa ne a daidai lokacin da tulin Jami'o'in da suke kasar ke kuka kan rashin kayan aiki da kuma ingancin walwalar malamai.

A sashe na biyu na kudirin ya ce idan aka samar da Jami'ar, za ta inganta koyarwa ba tare da bambancin jinsi da launin ko kuma siyasa ba da fuskar samun ilimi da bangaren harsunan gida da al'adu.

Yadda tsarin Jami'ar Tinubu za ta kasance

Za a ba daliban da suka kammala karatun satifiket na 'Diploma da Digiri har da bincike mai zurfi tare da koyon sana'o'i.

Kudirin ya tsallake karatu na farko inda ake sa ran nan da makwanni zai tsallake karatu na biyu tare da jin ra'ayin al'umma da masu ruwa da tsaki daga bisani.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

An fadi halin da Tinubu ke ciki

Mun baku labarin cewa hadimin Shugaba Bola Tinubu a bangaren siyasa, Ibrahim Masari ya yi magana kan rade-radin rashin lafiyar shugaban.

Masari ya yi fatali da jita-jitar inda ya ce Tinubu lafiyarsa kalau kuma yana cikin koshin lafiya a inda ya ke hutu.

Hadimin ya shawarci masu yada jita-jitar da su yi hakuri da lafiya da rashinta duka na hannun Ubangiji mahalicci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.