Rashin Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Fadi Halin da Ake Ciki

Rashin Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Fadi Halin da Ake Ciki

  • Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya taɓo batun matsalar rashin tsaron da ta daɗe tana ci wa jihar tuwo a ƙwarya
  • Gwamna Dauda ya ce gwamnatinsa na bakin ƙoƙarin ta domin ganin ta kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar
  • Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da gwamnatin ke yi domin shawo kan matsalar rashin tsaro, lamarin yana hannun Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce ana samun ci gaba kan matsalar tsaro a jihar sakamakon kashe wasu shugabannin ƴan ta’adda.

Gwamna Dauda ya ce duk da cewa gwamnatinsa na yin iya ƙoƙarinta na ganin ta kawar da ƴan bindiga, amma a ƙarshe makomar mutane tana hannun Allah.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya yi alhinin kisan jami'an tsaro, ya ba da tabbaci

Gwamnan Zamfara ya koka kan rashin tsaro
Gwamna Dauda Lawal ya ce lamarin rashin tsaro a Zamfara yana hannun Allah Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamna Dauda ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a bayan ya sanya labule da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a fadar Aso Rock Villa, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Zamfara ya magantu kan rashin tsaro

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa na yin iyakar bakin ƙoƙarinta domin magance matsalar rashin tsaron, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

"Muna yin iya ƙoƙarinmu wajen ganin mun tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’armu, amma komai yana hannun Allah"
"Maganar gaskiya ita ce, an shafe shekaru 12 ana fama da matsalar rashin tsaro a jihar Zamfara, kuma a matsayinmu na gwamnatin da ta san ya kamata, muna tunkarar matsalar."
"Muna yin iya ƙoƙarinmu don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin mutanenmu. Wannan abu ne wanda za mu ci gaba da yi har sai mun kawo ƙarshen wannan matsalar ta’addanci a Zamfara."

Kara karanta wannan

Jerin 'yan Kannywood 8 da suka rabauta da mukami a gwamnati bayan zaben 2023

"Ina addu'ar cewa ko gobe ma mutanen Zamfara za su yi barci cikin aminci. Muna yin iyakar abin da za mu iya, amma lamarin yana hannun Allah."

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Dauda ya yi alhinin kisan jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi alhinin rasuwar jami’an tsaron rundunar Askarawan Zamfara da aka kashe a jihar.

Wasu miyagun bindiga ne suka kashe jami'an tsaron a wani harin kwantan ɓauna da suka kai a yankin Tsafe na jihar Zamfara. Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng