Ta Leko Ta Koma: Gwamna Ya Musanta Amincewa da Mafi Karancin Albashin N70,000
- Ma'aikatan gwamnatin jihar Jigawa sun ga samu sun ga rashi kan sabon mafi ƙarancin albashin N70,000 da aka amince da shi
- Gwamna Malam Umar Namadi ya musanta amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin wanda tun da farko hadiminsa ya sanar da amincewarsa
- Hadimin gwamnan dai ya fito ya janye kalaman da ya yi na cewa Gwamna Namadi ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin ga ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Ma’aikatan gwamnatin jihar Jigawa sun shiga ruɗani yayin da gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya musanta amincewa da mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Tun da farko dai babban mai ba Gwamna Namadi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Malam Ado Kazaure, ya sanar da amincewa da mafi ƙarancin albashin.
Murna ta kom ciki ga ma'aikata
Jaridar Tribune ta ce ma'aikata sun yi matuƙar farin ciki kuma sun nuna murnarsu a shafukan sada zumunta bayan da labarin ya ɓarke a ranar Alhamis 10 ga watan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ma’aikatan gwamnati sun shiga ruɗani da takaici bayan wani saƙon faifan murya, daga babban mai ba da shawara kan harkokin albashi da fansho, Ado Kazaure, inda ya janye kalamansa, ya kuma musanta amincewar gwamnan.
Gwamnati ta musanta amincewa da N70,000
Lokacin da aka tuntuɓi Ado Kazaure domin tabbatar da sahihancin faifan sautin muryar inda ya musanta amincewa da mafi ƙarancin albashi na N70,000, ya tabbatar da sahihancinsa da abin da ke cikinsa.
"Eh gaskiya ne, ni ne na yi magana. Jin da kuka yi daga gidan rediyon jihar Jigawa ya tabbatar muku ni ne."
- Malam Ado Kazaure
Bai ƙara cewa komai ba sannan sai ya katse kiran da sauri.
Gwamna Namadi ya siya jami'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar zartaswan jihar Jigawa ta amince da sayen wata jami'a mai zaman kanta mai suna Jami'ar Khadija da ke garin Majia.
Majalisar ta amince da sayen jami'ar ne a wani ɓangare na manufofi 12 na Gwamna Umar Namadi wanda ya ƙunshi bunƙasa harkokin ilimi a Jigawa.
Asali: Legit.ng