Watanni da Maido Shi Mulki, Sanusi II Zai Nada Kawun Gwamna Abba a Sarauta

Watanni da Maido Shi Mulki, Sanusi II Zai Nada Kawun Gwamna Abba a Sarauta

  • Muhammadu Sanusi II ya amince da yin nadin sarauta ga wasu gidaje da su ka yi mulki ko su ka rike sarauta a baya
  • An zabi Abba Yusuf daga gidan Galadiman Kano ya zama Dan makwayon Kano, za a nada shi ranar 18 ga watan Oktoba
  • Tun shekarar 1965 rabon da a samu wani a cikin zuri’arsu da ya rike sarauta sai da Muhammadu Sanusi II ya dawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kammala shirye-shiryen yin nadin wasu sarauta a fadarsa.

Daga cikin wadanda Khalifa Muhammadu Sanusi II zai nada a karshen mako mai zuwa har da Alhaji Abba Yusuf.

Muhammadu Sanusi II zai nada Alhaji Abba Yusuf a matsayin sabon Danmakwayon Kano
Muhammadu Sanusi II zai nada Abba Yusuf Danmakwayon Kano Hoto: Muhammad Sanusi II Study Snippets/SarautaTV
Asali: Facebook

Muhammadu Sanusi II zai nada sarauta

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi illar gobarar kasuwa ga Kano, Abba ya yi wa 'yan kasuwa alkawari

Sanarwa ta fito daga shafin Muhammadu Sanusi II Study Snippets a dandalin X a game da shirin nadin sarautar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya na farin cikin gayyatar al’umma zuwa nadin sabon Dan makwayon Kano; Alhaji Abba Yusuf"

- Sanarwa

Sanusi II zai ba Kawun gwamna sarauta

Kamar yadda bayanin ya nuna, wanda za a nada Dan makwayon Kano kawu ne ga Mai girma gwamnan Kano.

Bayan kasancewarsa kawu, an ce Abba Yusuf suruki ne ga gwamna Abba Kabir Yusuf da ya karbi mulki a 2023.

A ranar 18 ga watan Oktoba zai zama sabon Dan Makwayon Kano, Daily Trust ta ce mahaifinsa ya rike sarautar a da.

Meyasa Sanusi II zai ba kawun gwamna sarauta?

Wannan ya na cikin kokarin da Sanusi II yake yi wajen yin nadi ga ‘ya ‘ya da jikokin sarakunan da aka yi a baya.

Kara karanta wannan

Gobara: Daga dawowa Kano, Aminu Ado Bayero ya ziyarci Kantin Kwari

Tarihi ya ce rabon da a samu wanda ya rike sarauta daga gidan Galadiman Kano Yusuf kusan shekaru 60 kenan.

Galadima Yusuf ya na cikin ‘ya ‘yan Sarki Maje Karofi kuma ya jagoranci yakin basasa da aka yi kuma sun yi nasara.

Sai dai Yusuf bai yi mulki ba domin Allah SWT ya yi masa cikawa bayan yakin.

Sanusi II ya kuma tuna da jikokin Sarki Maje Ringim, Sarki Tukur da na Waziri Ahmadu da yam utu a yakin basasan.

Wani nadin da ya ja hankali shi ne na kusa da Sanusi II, Alhaji Munir Sanusi Bayero wanda zai zama Wamban Kano.

Ribadu ya kara tada wutar rikicin sarautar Kano

Kwanaki aka ji aka ji labari an ga Aminu Ado Bayero a taro, har mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro ya kira shi Sarki.

Ashraf Sanusi Lamido ya na ganin an yi banza tun da Nuhu Ribadu a tsarin mulki, bai da ikon nada wanda zai yi sarauta a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng