Gwamnan APC Ya Tsallake Gida, Ya ba Nijar N16m na Gyaran Masallaci Mai Shekaru 200

Gwamnan APC Ya Tsallake Gida, Ya ba Nijar N16m na Gyaran Masallaci Mai Shekaru 200

  • Gwamnatin jihar Katsina ta tallafawa garin Damagaram da ke kasar Nijar da makudan kudi domin gyaran masallaci
  • Gwamna Umaru Dikko Radda ya ba da gudunmawar $10,000 na gyaran masallacin da ya kai shekaru 200 da kafuwa a duniya
  • Sultan na Damagaram, Alhaji Abubakar Sanda-Umaru ya yabawa gwamnan inda ya ce hakan zai kara musu dankon zumunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Gwamna Umaru Dikko Radda ya tallafa da makudan kudi saboda gyaran masallaci a kasar Nijar.

Gwamna Radda ya ba da gudunmawar $10,000 domin gyaran masallaci da ya kai shekaru 200 a Damagaram da ke Nijar.

Gwamna ya tallafa da N16m domin gyaran masallaci a Nijar
Gwamnan Katsina, Umaru Dikko Radda ya ba garin Damagaram a Nijar gudummawar N16m domin gyaran masallaci. Hoto: Umaru Dikko Radda.
Asali: Facebook

Gwamna Radda ya ba Nijar N16m domin gyaran masallaci

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya shiga matsala da ɗan Majalisa ya maka shi a kotu da hadimansa 2

Hadimin gwamnan a bangaren siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo shi ya bayyana haka a Katsina a cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwajo-gwajo wanda ya mika gudunmawar ya ce a kwanan baya masallacin ya rushe wanda yanzu za a gyara shi bayan shafe tsawon lokaci.

Hadimin wanda ke riƙe da mukamin Turakin Damagaram ya mika gudunmawar wanda ya zarce N15m a kudin Najeriya.

Sarkin Damagaram ya godewa gwamna kan gudunmawa

Ya ce Sultan na Damagaram, Alhaji Abubakar Sanda-Umaru ya godewa gwamnan game da gudunmawar da ya bayar inda ya ce tabbas ya taimaka matuƙa gaya.

Basaraken ya ce wannan zai kara dankon zumunci tsakanin Katsina da Damagaram da suka shafe shekaru 500 suna yi.

Gwajo-gwajo ya fadawa basaraken cewa Gwamna Radda ya ba da gudunmawar saboda yadda ya ke don ganin al'umma ta samu cigaba ta kowane fanni.

Kara karanta wannan

"A kasa su ke zaune:" Gwamna ya koma makarantar mata a Kano da kayan aiki

Sokoto: Gwamna zai gyara masallatai kan N95.4m

Kun ji cewa Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya ware makudan kudi domin gyaran masallatan Juma'a a jihar.

Gwamnan ya ware makudan kudi har N95.4m domin gyaran masallatan Juma'a 87 a fadin jihar baki daya wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.

Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin gwamnan da ware biliyoyin kuɗi kan ayyukan da ba su cancanci lakume makudan kudi kamar haka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.