"A kasa Su ke Zaune:" Gwamna Ya Koma Makarantar Mata a Kano da Kayan Aiki
- Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin da ya dauka tun a watan Yuni na kai kayan inganta ilimi a makarantar 'Governors' College'
- An hango dalibai a cikin wani bidiyo su na nuna farin cikin yadda gwamnan ya taka har makarantar domin kai masu kayayyakin
- A kalamansa, gwamna Abba ya ce ya na kan akidar inganta baki daya bangaren ilimi domin inganta rayuwar yaran jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - A ranar Juma'ar nan gwamna Abba Kabir Yusuf ya shige gaba zuwa makarantar 'Governors' College' domin kai kayan karatu.
Gwamnan ya ziyarci makarantar a watan Yuni inda ya bayyana takaicin halin da ya ga daliban a ciki na rashin kayan ba su ilimi mai inganci.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, an hango gwamnan a cikin dalibai inda ya bayyana jin dadi kan yadda ya iya cika alkawarin da ya dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya kai kujeru makaranta
Sanusi Bature Dawakin Tofa, darakta janar kan yada labaran Abba Kabir Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnan ya kai kayan aiki 'Governors' College'.
Daga cikin kayayyakin da gwamnan ya jagoranci kai wa akwai kujerun zaman dalibai 1,000 domin ya tarar da dalibai na zaune a kasa a watannin baya.
"Za mu gyara ilimi a Kano:" Gwamna Abba
Gwamnatin Kano ta kara jaddada kudirin da ta dauko na fargado da ilimi a fadin jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta yi wasa da ilimi ba, tare da cewa za a inganta yanayin koyo da koyarwa a jihar.
Gwamna Abba ya zama Gwarzo kan ilimi
A wani labarin kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga jerin gwamnoni biyar a kasar nan da aka tabbatar su na abin da ya dace wajen inganta ilimi.
Kungiyar malamai ta kasa (NUT) da hadin gwiwar ma'aikatar ilimi ta tarayya ne suka zakulo gwamnonin kasar nan da ake ganin sun taka muhimmiyar rawa kan ilimi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng