Amaechi: Kalaman Ministan Buhari Sun Yi wa APC Zafi, An Zarge Shi da Tada Hargitsi

Amaechi: Kalaman Ministan Buhari Sun Yi wa APC Zafi, An Zarge Shi da Tada Hargitsi

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zargi tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari da rashin kishin kasa
  • Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana mamaki kan yadda yan kasa su ka zuba ido ana karin farashin fetur
  • A makon da ya ke karewa ne kamfanin mai na kasa NNPCL ya kare farashin litar fetur zuwa sama da N1,000 a gidajen kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fusata da kalaman tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi tare da zarginsa da kokarin tunzura jama'a.

APC ta kuma zargi tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi da rashin kishin kasa ko son zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Mutane 16 ‘yan gida 1 da suka shiga fagen siyasa kuma suka shahara a Najeriya

Tibubu
Gwamnati ta zargi Rotimi Amaechi da rashin kishin kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A sakon da hadimin shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, APC ta zargi Rotimi Amaechi da zama dan ci ma zaune a siyasar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta bayyana mamaki kan yadda hankali ke zuwa ga yan adawa idan sun bar mulki.

Gwamnati ta zargi Amaechi da lalata kasa

A sakon da APC ta fitar wanda hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya yada a yammacin yau Juma'a, an zargi Amaechi da rayuwa da 'satar' kudin gwamnati.

APC ta ke gatse cewa tun a zamanin da Amaechi ke gwamnan Ribas har ya zama shugaban majalisa da kuma Minista, ba abin da ya sani sai cinye kudin jama'a.

APC ta caccaki yan adawar Tinubu

APC mai ci ta zargi yan adawa irinsu Atiku Abubakar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Peter Obi da Rotimi Amaechi da yi wa kasa bakin ciki.

Kara karanta wannan

Neman beli: Kotu ta kara hankaɗa keyar jami'in Binance zuwa kurkuku

Hadimin Tinubu kan kafafen yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ne ya wallafa sakon da Sakataren yada labaran APC, Felix Morka ya sa wa hannu.

Karin farashin fetur: An caccaki gwamnatin Tinubu

A wani labarin kun ji yadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da rashin damuwa da halin matsin rayuwa da ake ciki.

Atiku Abubakar ya ce Tinubu ya zama 'TPain',wato mai jawo wa kasa wahala, inda ya ce gwamnati ba ta da makama kan tsarin farashin fetur a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.