'Ba Laifinsa ba ne', Ndume Ya Fadi Nufin Tinubu, Ya Roki Alfarma bayan Tsadar Fetur

'Ba Laifinsa ba ne', Ndume Ya Fadi Nufin Tinubu, Ya Roki Alfarma bayan Tsadar Fetur

  • Sanatan Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume ya roki alfarma wurin shugaba Bola Tinubu kan halin kunci da ake ciki
  • Ndume ya ce tabbas ya sani Tinubu yana da kyawawan tsare-tsare da nufin alheri ga kasar, sai ya zargi mukarrabai da laifi
  • Sanatan na APC ya bukaci Tinubu da ya yi duba zuwa ga halin kunci da yan Najeriya ke ciki, ya ce abin ya wuce misali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanata Mohammed Ali Ndume ya yi magana bayan kara farashin man fetur a Najeriya.

Ndume ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya janye wannan kari da ya yi, ya ce yan Najeriya suna cikin mummunan hali.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Sanatan APC ya shawarci Tinubu kan karin farashin man fetur
Sanata Ali Ndume ya koka kan halin kunci da yan Najeriya ke ciki. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Sen. Mohammed Ali Ndume.
Asali: Facebook

Sanata Ndume ya yabawa tsare-tsaren Tinubu

Sanatan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume ya ce tabbas Tinubu yana da kyakkyawan tsari ga yan Najeriya wasu ne ke neman kawo cikas, Punch ta ruwaito wannan.

Sanatan Borno ta Kudu ya ce akwai wadanda ke ba Tinubu gurguwar shawara domin biyan buƙatar kansu.

Ndume ya roki Tinubu kan halin kunci

"A karan kai na, na san Bola Tinubu yana nufin Najeriya da alheri saboda na san waye shi."
"Sai dai akwai wasu mukarrabansa wadanda ba su kishin kasa a zuciyarsu da ke ba shi gurguwar shawara."
"Ina rokonsa da ya yi watsi da wadannan mutane ya duba halin da al'umma ke ciki na tsadar rayuwa."

Kara karanta wannan

Kusa ya bayyana gaskiyar abin da ya kai Tinubu Birtaniya yayin da ake rade radi

- Sanata Ali Ndume

Ndume ya bukaci Tinubu da ya duba lamarin da za ran ya dawo kasa Najeriya saboda mutane sun shiga yanayin talauci da yunwa.

Sanata Ndume ya soki sojoji kan ta'addanci

Kun ji cewa Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya koka kan yadda ta'addanci ke kara kamari tare da gagara kawo karshensu.

Ndume ya bayyana cewa a karshen mulkin Goodluck Jonathan ya yi nasarar fatattakar yan ta'addan Boko Haram.

Ndume ya nuna damuwa game da yadda hafsoshin tsaro suka gagara kawo karshen dan ta'adda, Bello Turji bayan tsawon lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.