Janar TY Danjuma Ya Yi Barazanar Maka Malamin Addini a Kotu, Ya Ba Shi Wa'adi

Janar TY Danjuma Ya Yi Barazanar Maka Malamin Addini a Kotu, Ya Ba Shi Wa'adi

  • Wani Fasto mai suna Paul Rika ya shiga matsala bayan wallafa wani littafi da ake zargin ya keta alfarmar Theophilus Danjuma
  • Tsohon hafsan tsaron sojoji, TY Danjuma ya koka kan yadda aka wallafa wasu bayanai da ke cin mutuncinsa da kimarsa
  • Danjuma ya gargadi Faston da ya cire rubutun da ya yi a wasu shafukan littafin, kuma ya ba shi wa'adin kwanaki bakwai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Janar Theophilus Danjuma mai ritaya ya yi barazanar maka malamin addinin Kirista a kotu.

Tsohon hafsan tsaro ya nuna damuwa game da wallafa wani littafi da Fasto Paul Rika ya yi inda ya nemi diyyar N1bn.

Kara karanta wannan

Neman beli: Kotu ta kara hankaɗa keyar jami'in Binance zuwa kurkuku

TY Danjuma ya yi barazana ga malamin addini
Janar Theophilus Danjuma zai maka Fasto a kotu kan cin mutuncinsa. Hoto: TY Danjuma Foundation.
Asali: Facebook

TY Danjuma na zargin an bata masa suna

Punch ta ce Danjuma na zargin akwai wasu bayanai a shafukan littafin da suka ci zarafinsa da zubar da kimarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan wallafa littafin da Faston ya yi mai suna 'Sakon Ubangiji ga kabilar Kuteb da yan asalin jihar Taraba'.

TY Danjuma ta bakin lauyansa, Tayo Oyetibo ya ba Faston mako daya ya cire bayanan game da attajirin a cikin littafin.

Janar Danjuma mai ritaya ya ce ya samu bayanin littafin ne da aka wallafa a watan Satumbar 2024 a wurin yaransa da suka siya.

TY Danjuma ya ba Fasto wa'adin kwanaki 7

"Mun samu bayanai kan wani littafi da Fasto Paul Rika ya wallafa mai suna 'Sakon Ubangiji ga kabilar Kuteb da yan asalin jihar Taraba'."
"Wannan wallafa ta jawowa Danjuma rashin kwanciyar hankali inda ya shiga wani irin hali duba da kallon da al'umma ke yi masa bayan wallafa littafin."

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

- Cewar sanarwar

Lauyoyin TY Danjuma sun ba Faston kwanaki 90 domin ya sake sauya littafin da buga shi tare da ba shi hakuri kan abin da ya yi.

TY Danjuma ya yi alhinin rasuwar amininsa

A baya, kun ji cewa tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma ya bayyana cewa ya so a ce shi ya mutu kafin amininsa.

Theophilus Danjuma ya bayyana haka a wajen taron jinjina da bankwana ga tsohon jakadan Najeriya a Rasha, Dan Suleiman.

A cewar Janar Danjuma mai ritaya, bisa al'ada, shi ya kamata a ce abokinsa kuma kaninsa ya birne ba wai akasin haka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.