Neman Beli: Kotu Ta Kara Hankaɗa Keyar Jami’in Binance Zuwa Kurkuku

Neman Beli: Kotu Ta Kara Hankaɗa Keyar Jami’in Binance Zuwa Kurkuku

  • Kotun tarayya ta zauna domin cigaba da shari'ar jami'in kamfanin Binance bisa zargin ketare biyan haraji da ake yi masa
  • Alkalin kotun, Mai shari'a Emeka Nwite ya ki amincewa da neman belin Tigran Gambaryan da lauyansa ya yi kan rashin lafiya
  • Mai shari'a Emeka Nwite ya lissafa dalillai da suka sanya kotun hana belin Tigran Gambaryan duk da ikirarin rashin lafiya da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kotun tarayya a Abuja ta cigaba da sauraron shari'ar da EFCC ta shigar da kamfanin Binance.

A zaman kotun na yau, mai shari'a Emeka Nwite ya ki amincewa da belin Tigran Gambaryan da lauyansa ya nema.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

Binance
Kotu ta hana belin jami'in Binance. Hoto: @OfficialEFCC, @Naija_PR
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Gambaryan ya nemi belin makonni shida ne damin a samu a duba lafiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kan me aka zargin kamfanin Binance?

Hukumar tattara haraji ta FIRS ta yi zargin cewa kamfanin Binance ya gaza yin rajista da ita wanda hakan ya jawo tuhuma har ta Dala miliyan 35.4.

Haka zalika FIRS ta yi zargin kamfanin bai gabatar da shaidar ayyukan da yake yi na hada-hadar kasuwanci balle a tantance nawa yake samu wajen biyan haraji.

A kan haka ne hukumar EFCC ta cafke Tigran Gambaryan kuma ta gabatar da shi a gaban kotu domin a masa hukuncin da ya dace da laifin da ake zarginsa da shi.

An hana jami'in kamfanin Binance beli

Lauyan jami'in kamfanin na Binance ya bukaci a ba shi damar tafiya jinya na tsawon makonni shida saboda uzurin rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

Daily Post ta wallafa cewa lauyan EFCC ya ki amincewa da lamarin inda ya ce an kai shi asibitoci ciki har da asibitin fadar shugaban kasa.

A karshe, alkalin kotun ya ki amincewa da belin Tigran Gambaryan kuma an daga shari'ar zuwa ranar 18 ga watan Oktoban 2024.

Gambaryan ya shigar da EFCC kara

A wani rahoton, kun ji cewa an shigar da ƙarar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu da EFCC.

Babban jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, ya kai ƙarar Nuhu Ribadu da hukumar EFCC bisa zargin tauye masa haƙƙinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng