Gwamnati Ta Fara Sayar da Buhun Shinkafa a kan N40,000 a Jihohi

Gwamnati Ta Fara Sayar da Buhun Shinkafa a kan N40,000 a Jihohi

  • Gwamnatin tarayya ta fara da jihar Ogun wajen karya farashin shinkafa inda za a rika sayar da buhu a kan N40,000 kacal
  • A ranar Alhamis ma'aikatar noma ta samar da abinci ta kasa ta kaddamar da sayar da shinkafa mai rahusa a birnin Abeokuta
  • Gwamnatin tarayya ta bayyana sharudan da al'umma za su cika kafin samun shinkafar da aka samar domin kawo sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin sayar da shinkafa a farashi mai rahusa a jihohin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Alhamis ne aka ƙaddamar da shirin a jihar Ogun kafin fara shi a sauran jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sarkin Musulmi ya fada wa yan Najeriya abin da za su yi wa shugabanni

Bola Tinubu
An fara sayar da shinkafa a jihohi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Ahmad Sabo
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa daraktan ma'aikatar noma da samar da abinci ne ya wakilci ministan noma, Sanata Abubakar Kyari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara sayar da buhun shinkafa a N40,000

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin sayar da buhun shinkafa a kan N40,000 a Abeokuta na jihar Ogun.

Ma'aikatar noma ta bayyana cewa za a yi adalci wajen tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta ne suke sayen shinkafar.

Sharadin sayen buhun shinkafar N40,000

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa duk wanda zai saye shinkafar dole ya nuna lambar shaidar zama ɗan kasa ta NIN.

Haka zalika masu sayen shinkafar za su zo da katin banki na ATM da za a zare kudin saboda ba kudi a hannu za a yi cikin ba.

Dalilin fara sayar da shinkafa a Ogun

Ma'aikatar noma ta bayyana cewa fara da jihar Ogun ne kasancewar yadda gwamna Dapo Abiodun ya ke nuna salon shugabanci mai kyau.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

Rahoton Channels Television ya nuna gwamna Dapo Abiodun ya mika godiya ga shugaba Bola Tinubu kan kawo shirin sayar da shinkafar.

An yi kaca-kaca da Tinubu kan tashin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Laraba da ta wuce ne kamfanin NNPCL ya yi karin kudin man fetur ana tsaka da wahalar rayuwa.

Lamarin ya tayar da kura musamman tsakanin masu karamin karfi kuma yan siyasa ciki har da Atiku Abubakar sun yi martani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng