Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Fada wa Yan Najeriya Abin da za Su Yi Wa Shugabanni

Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Fada wa Yan Najeriya Abin da za Su Yi Wa Shugabanni

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bayar da hanyar da za a bi da shugabannin da ke mulki a Najeriya
  • Sarkin Musulmi ya ba mutane shawarar gujewa tsinewa shugabanni da sauran jagororin kasar nan duk da halin da ake ciki
  • Ya bayyana matsayarsa yayin taron kaddamar da littafin da aka rubuta kan shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oleyede

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kwara - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya ba yan Najeriya shawara kan abin da ya kamata su rika yi wa shugabanninsu.

Sultan ya bayar da shawarar a jami'ar Ilorin a taron kaddamar da littafi da aka rubuta kan shugaban hukumar jarrabawar JAMB, Farfesa Ishaq Oleyede.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara sayar da buhun shinkafa a kan N40,000 a jihohi

Sultan
Sarkin Musulmi ya ba da shawara kan daina tsinewa shugabanni Hoto: Sultan of Sokoto TV
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro Mai alfarma Alhaji Sa'ad Abubakar III na cewa a duk halin da za a tsinci kai, ba ya dacewa a rika tsinewa shugabanni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi ya hana tsinewa shugabanni

BBC Hausa ta wallafa cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce duk lalacewar shugaba, bai dace talakawansa su rika tsine masa ba.

Mai alfarma Sarkin Musulmin na bayar da shawarar a lokacin da yan kasar nan su ka fusata da yadda gwamnati ke kallonsu a cikin matsin rayuwa.

"A yi wa shugabanni addu'a:" Sarkin Musulmi

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce dukkanin shugabannin kasar nan na bukatar jama'a su rika sanya su a cikin addu'o'in fatan alheri a shugabanci.

Mai alfarman ce sam babu kyau wadanda ake jagoranta su rika fadin munanan kalamai a kan shugabanninsu duk da lalacewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Farashin fetur: Atiku ya yi wa Tinubu sabon lakabi, ya zarge shi da kuntata wa jama'a

Sarkin Musulmi ya gargadi shugabanni

A baya mun wallafa cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ja kunnen yan siyasa da sauran shugabanni kan zagi da ci wa junansu fuska saboda sabanin ra'ayi.

Sarkin Musulmi ya yi gargadin lokacin da ya karbi bakuncin Atiku Abubakar a sa'ilin da ya ke neman takarar shugaban kasa, tare da ba su shawarar su gyara lahirarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.