Ta Faru Ta Kare: Majalisa Ta Yi Albishir ga Yan Kasa kan Saukar Farashin Fetur

Ta Faru Ta Kare: Majalisa Ta Yi Albishir ga Yan Kasa kan Saukar Farashin Fetur

  • Majalisar dattawa ta bayyana cewa kamata ya yi kasuwar fetur ta rika yi wa kanta farashi tun bayan janye tallafi a bangaren
  • Kamfanin mai na kasa (NNPCL) dai ya kara wa masu sayen fetur a gari da yan kasuwa farashi zuwa sama da N1,000 a kowace lita
  • Shugaban majalisa, Godswill Akpabio ya ce su na sa ido kan karin farashin da halin da jama'ar gari ke ciki kuma za a dauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya tofa albarkacin bakinsa kan karin farashin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

A ranar Laraba ne kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya fara sayar da kowace litar fetur a kan sama da N1,000 ba tare da bayanin dalilin karin ba.

Majalisa
Majalisar dattawa na sa ido kan karin farashin fetur Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa shugaban majalisar, Godswill Apkabio ya ce matsalar yawan kara farashin litar fetur zai zo karshe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An daina karin farashin fetur:" - Majalisa

Channels Television ta wallafa cewa Sanata Godswill Akpabio ya ce ana sa ran ba za a ci gaba da samun karuwar farashin fetur ba tun da an kammala janye tallafi.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke kaddamar da cibiyar yan jarida ta majalisar dattawa da aka yi wa kwaskwarima a babban birnin tarayya Abuja.

Majalisa za ta shiga maganar man fetur

Shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da kasuwar fetur za ta rika yi wa kanta farashi.

Kara karanta wannan

Ana wayyo da karin farashin fetur da NNPCL ya yi, IPMAN za ta ballo ruwa

Ya kara da cewa majalisa na bibiyar halin da ake ciki kan karin da NNPCL ya yi a kwanan nan, kuma za su shiga tsakani idan akwai bukatar hakan.

IPMAN ta zargi NNPCL da hana ta fetur

A baya mun ruwaito cewa kungiyar dillalan fetur (IPMAN) ta yi barazanar tsunduma yajin aiki bayan kamfanin NNPCL ya hana ta mai duk da ta biya kudi.

Sakataren yada labaran IPMAN na kasa, Chinedu Ukadike ya ce baya ga hana su fetur da kamfanin NNPCL ya yi, ya na kuma sayar masu da tsada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.