Tarin Yan Bindiga Sun Nufo Kano bayan an Fatattake Su daga Zamfara

Tarin Yan Bindiga Sun Nufo Kano bayan an Fatattake Su daga Zamfara

  • Rahotanni na nuni da cewa yan bindiga da aka matsawa lamba a jihar Zamfara sun fara tserewa zuwa wasu yankunan Arewa
  • Wani bincike ya gano cewa wasu daga cikin yan bindigar sun koma neman mafaka a Kano bayan wuta da suka sha a Zamfara
  • An bayyana wasu daga cikin unguwannin da ake zargin mafi yawan yan bindigar suna zaune a cikin garin Kano da suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Ana tsoron cewa wasu daga cikin yan bindiga da aka matsawa lamba sun fara neman mafaka Kano.

Hakan na zuwa ne bayan jami'an tsaron Najeriya sun zafafa luguden wuta a kan miyagun a yankunan jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

An ceto mutane wajen yan bindigar da suka ƙona dan sanda a kasuwa

Jihar Kano
Yan bindiga sun fara neman mafaka a Kano. Hoto: Legit
Asali: Original

Rahoton RFI Hausa ya nuna cewa tun farkon makon nan aka mika labarin ga gwamnatin jihar Kano domin ɗaukar mataki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miyagun yan bindiga sun nufo jihar Kano

Jaridar the Guardian ta fitar da rahoto kan cewa wasu yan bindiga da aka matsawa lamba a Zamfara sun fara komawa Kano.

Rahoton ya nuna cewa dama wasu daga cikin yan bindigar na zama a Kano sai su rika taimakawa miyagu yan uwansu a sauran jihohi.

Wasu wuraren yan bindiga ke zaune a Kano?

Ana zargin cewa wasu yan bindigar sun mallaki gidajen zama a jihar Kano tsawon shekaru da suka gabata.

A yanzu haka ana cewa sun nemi mafaka a Rijiyar Zaki, Tudun Yola, Ɗorayi Babba, Rijiyar Lemo da Yan Awaki.

Za a fara zakulo yan bindiga a Kano

Wata majiya ta sanar da cewa tun a ranar Litinin da ta wuce aka mika rahoto ga gwamnatin jihar Kano kan lamarin.

Kara karanta wannan

Matasa sun ba shi guba, sun caccakawa mai gidansu wuƙa, sun ƙona gawarsa ƙurmus

Haka zalika an sanar da cewa jami'an tsaro sun fara aiki domin ganin an zakulo miyagu yan bindigar cikin gaggawa.

An kashe babban dan bindiga a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojoji ta samu gagarumar nasara kan yan ta'adda da sauran miyagu a jihohi daban daban a mako daya.

A jihar Jigawa da ke yankin Arewacin Najeriya, sojojin sun yi nasarar hallaka jagoran yan ta'adda da ke kira Mai Hijabi bayan sun fafata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng