Ana Wayyo da Karin Farashin Fetur da NNPCL Ya Yi, IPMAN za Ta Ballo Ruwa

Ana Wayyo da Karin Farashin Fetur da NNPCL Ya Yi, IPMAN za Ta Ballo Ruwa

  • Dillalan man fetur na kasa sun fara fusata da yadda kamfanin mai na kasa (NNPCL) yake yi masu wasa da hankali
  • Kungiyar 'yan kasuwar ta zargi NNPCL da watsi da ba su fetur duk da kuwa an shafe watanni da biyan kudin ga kamfanin
  • Sakataren yada labaran kungiyar IPMAN ya bayyana cewa su na shirin daukar mataki kan abin da NNPCL yake yi masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Rashin samun fahimtar juna tsakanin kamfanin mai na kasa (NNPCL) da dillalan fetur zai iya jawo sabuwar matsala kan samuwar mai.

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta zargi kamfanin NNPCL da hana ruwa gudu wajen samuwar man fetur duk da sun bayar da kudinsu.

Kara karanta wannan

'A fita zanga zanga,' Yadda aka yi rubdugu ga Tinubu kan tashin kudin fetur

NNPCL
IPMAN ta yi gargadin shiga yajin aiki Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Sakataren yada labaran IPMAN na kasa, Chinedu Ukadike ya ce za su dauki mataki kan abin da NNPCL ke masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fetur: Kungiyar IPMAN za ta shiga yajin aiki

Daily Post ta wallafa cewa kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta ce za ta iya tsunduma yajin aiki ta hanyar rufe gudajen mansa da ke kasar biyo bayan rashin biya masu bukatunsu.

IPMAN ta zargi kamfanin NNPCL da hana shi fetur duk da an biya kudi tun watannin baya, sannan kuma ana sayar masu da tsada a halin yanzu.

IPMAN na zargin NNPCL da hana man fetur

Dillalan man fetur a kasar nan sun zargi kamfanin NNPCL da hana su fetur watanni da biyansu kudi.

Kungiyar dillalan ta kasa ta kuma bukaci kamfanin ya dawo masu da kudin da su ka biya, wanda ake fargabar zai kara jawo karuwar wahalar fetur a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta yi albishir ga yan kasa kan saukar farashin fetur

Farashin fetur: IPMAN ta caccaki NNPCL

A wani labarin kun ji cewa kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa NNPCL ya sayar mata da kowace litar fetur a kan sama da N1,000.

Kungiyar ta bayyana haka ne jim kadan bayan NNPCL ya kara farashin fetur kuma ya tsame kansa daga zama mai dakon fetur daga matatar Dangote.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.