Wani Ƙusa Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ya Kai Tinubu Birtaniya yayin da Ake Rade Radi
- Kusa a siyasar Najeriya, Doyin Okupe ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya tafi Birtaniya domin kammala shirin sauya ministoci
- Tsohon kakakin shugaban kasar ya ce tafiyar Tinubu za ta dakile 'yan siyasa daga yin katsalandan a garambawul da za a yi wa ministocin
- Dakta Okupe wanda ya yi Allah wadai da masu sukar Tinubu kan zuwa Birtaniya, ya ce shugaban zai dawo gida da kyakkyawan albishir
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Dakta Doyin Okupe, ya yi magana kan hutun mako biyu da Shugaba Bola Tinubu ya je yi a kasar Birtaniya.
Dakta Doyin Okupe ya ce 'yan Najeriya da ke ce-ce-ku-ce kan tafiyar Tinubu Birtaniya ba su san abin da ke faruwa a kasar ba ne shi ya sa suke korafi.
Ana sukar Tinubu kan tafiya Birtaniya
Tsohon mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ranar Alhamis a Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi Allah wadai da irin sukar da ake yi wa shugaba Bola Tinubu saboda 'kawai' ya tafi kasar waje yin hutu maimakon ya zauna a kasar.
Tsohon darakta janar na yakin neman zaben shugaban kasa na Peter Obi ya ce:
“Na karanta soki-burutsun da mutane da dama ke yi game da tafiyar hutun da shugaban kasar ya yi zuwa kasar waje, kuma na fahimci rashin sani ne ya jawo haka."
"Abin da ya kai Tinubu Birtaniya" - Okupe
A mahangarsa, Dakta Doyin Okupe ya ce Tinubu ya tafi hutu Birtaniya ne domin ya nazarci yadda gwamnatinsa ta watanni 17 ta gudana, da kuma nemo mafita ga 'yan kasar.
“Haka kuma, Tinubu ya tafi hutun ne domin kauracewa katsalandan daga abokan siyasarsa kan shirinsa na yin garambawul a majalisar ministocinsa.
"Ya na da tabbacin cewa zamansa a Najeriya ba zai ba shi damar samun kwanciyar hankali da nutsuwar da ya ke bukata domin cimma burinsa ba."
Ya yi imanin cewa idan shugaban kasar ya kammala hutun mako biyun da ya je yi Birtaniya zai dawo da kyakkyawan albishir ga al'ummar Najeriya, inji rahoton Vanguard.
Zuwa yanzu Legit Hausa ta fahimci an fara yada jita-jita marasa tushe game da tafiyar da shugaban kasar ya yi zuwa Turai.
Tinubu ya shilla Birtaniya yin hutun mako
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya bar Abuja ne a ranar 2 ga watan Oktoba zuwa kasar Ingila domin fara hutun makonni biyu.
Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai ya ce Tinubu zai yi amfani da hutun domin yin nazari kan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng