Gwamna Zulum Ya Amince da Sabon Mafi Karancin Albashi, Ya Sa Lokacin Fara Biya
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata
- A cikin sanarwar da hadimin Zulum ya fitar, ya ce za a fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashin ne a watan Oktoban 2024
- Abdulrahman Ahmed Bundi ya ƙara da cewa gwamnan zai biya basussukan kuɗaɗen giratuti da ake bin gwamnatin Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya yi magana kan biyan ma'aikatan gwamnatin jihar sabon mafi ƙarancin albashi.
Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa jihar za ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi daga wannan watan na Oktoba.
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan kafafen yaɗa labaran zamani, Abdulrahman Ahmed Bundi, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum zai biya mafi ƙarancin albashi
Abdulrahman Bundi ya ce Gwamna Zulum ya yi taro da kwamitin aiwatar da mafi ƙarancin albashi na jihar, inda ya ba da umarnin a biya ma’aikatan gwamnati sabon albashin.
"An gudanar da taron ne a Maiduguri ranar Litinin a zauren majalisar da ke gidan gwamnati."
- Abdulrahman Ahmed Bundi
Zulum zai biya hakkokin ma'aikatan Borno
Hakazalika Abdulrahman Bundi ya ce Gwamna Zulum ya amince da fitar da N3bn domin biyan iyalan ma'aikatan da suka rasu a jihar Borno haƙƙoƙinsu.
Zulum ya kuma ba da tabbacin cewa zai biya basussukan kuɗaɗen giratuti da aka biyo jihar bashi tare da tabbatar da sake duba abin da ƴan fansho ke karba.
Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi
- Gwamna ya amince da karin albashi, ma'aikata za su samu fiye da N70,000
- Murna yayin da gwamna ya sanar da lokacin fara biyan mafi karancin albashi
- N70,000: Jerin gwamnonin Arewa da ke shirin fara karin albashi ma'aikata
Gwamna Zulum ya fara rabon tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Borno, Babagana Umaru Zulum, ya kaddamar da rabon kayan tallafi a hukumance ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.
Yayin ƙaddamar da shirin a Maiduguri, Farfesa Zulum ya ce za a fara rabon kayan tallafin da magidanta 5,235 a Gwange 1 da ke ƙaramar hukumar birni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng