Sojoji Sun Harbe Jagoran Yan Ta’adda ‘Mai Hijabi’, An Kashe Ƙarin Miyagu 165
- Rundunar sojoji ta samu gagarumar nasara kan yan ta'adda da sauran miyagu a jihohi daban daban cikin mako daya
- A jihar Jigawa da ke yankin Arewacin Najeriya, sojojin sun yi nasara hallaka jagoran yan ta'adda da ke kira Mai Hijabi
- Haka zalika rundunar sojin kasar a ta yi nasarar kwato tulin makamai da yan bindiga ke amfani da su wajen kai hare hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kashe babban ɗan ta'adda da ake kira Mai Hijabi.
Hakan na zuwa ne bayan farmaki da sojojin Najeriya suka kai kan miyagu a jihohi da dama na kasar nan.
Jaridar Punch ta wallafa cewa daraktan yada labarai rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ne ya fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakarun sojoji sun kashe dan ta'adda Mai Hijabi
Rahotanni sun nuna cewa sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da babban ɗan ta'adda da ake kira da Mai Hijabi a Jigawa.
An ruwaito cewa bayan sojoji sun fafata da mugun dan ta'addar kuma sun samu nasarar harbe shi har lahira.
Sojoji sun kashe miyagu 165 a jihohi
Cikin farmaki da sojojin Najeriya suka kai a jihohi sun samu nasarar kashe tarin yan ta'adda da suka kai 165 a cikin mako daya.
Tribune ta wallafa cewa rundunar sojin ta yi nasarar cafke yan ta'adda da miyagu 273 da kuma ceto mutane 188 da aka sace.
Sojoji sun kwato makamai a jihohi
A cikin nasarar da suka samu, sojojin Najeriya sun kwato bindigogi kirar AK47 guda 81 da tarin wasu makamai da harsashi.
Haka zalika sojojin sun kwato babura 21, motoci 19, wayoyin hannu 45, kudi N64,100 da sauran abubuwa da dama.
An kama yan bindiga a jihar Taraba
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun kama wasu muggan yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Taraba.
Bayan kama mutanen, sojojin sun kara samun nasarar cafke wani mai safarar makamai ga yan bindiga a karamar hukumar Lau ta jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng