Kotu Ta Yi Hukunci kan Sahihancin Kujerar Shugaban Majalisa da Kasafin Kudin N800bn

Kotu Ta Yi Hukunci kan Sahihancin Kujerar Shugaban Majalisa da Kasafin Kudin N800bn

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da Martins Amaewhule a matsayin halastaccen shugaban majalisar dokokin jihar Rivers
  • A hukuncin da kotun ta yanke na ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoban 2024, ta yi watsi da ƙarar Gwamna Siminalayi Fubara
  • Kotun ta soke kasafin kuɗin jihar Rivers na shekarar 2024 wanda Gwamna Fubara ya gabatar a gaban ƴan majalisa huɗu kacal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta tabbatar da Martins Amaewhule a matsayin sahihin shugaban majalisar dokokin jihar Rivers.

Kotun daukaka ƙarar ta yanke hukuncin ne yayin zamanta na ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoban 2024.

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar majalisar dokokin Rivers
Kotu ta tabbatar da Martins Amaewhule a matsayin shugaban majalisar Rivers Hoto: DeeoneAyekooto/officialPDPNig
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke

Kara karanta wannan

Gyara fadar Nasarawa: Kotu ta kawo cikas ga Aminu Ado Bayero, ta ba shi umarni

Kotun mai alƙalai uku ta kuma tabbatar da mambobin da ke ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule a matsayin halastattun ƴan majalisar dokokin jihar Rivers, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ɗaukaka ƙarar ta yi watsi da ƙarar da Gwamna Siminalayi Fubara ya shigar a gabanta, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Kotu ta soke kasafin kuɗin Rivers na 2024

Ta kuma amince da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a ranar 22 ga watan Janairu, wanda ya soke kasafin kuɗin jihar Rivers na shekarar 2024.

Kotu ta yi hukunci bisa cewa ba a gabatar da kundin kasafin kudin a gaban ƴan majalisar dokokin jihar waɗanda doka ta sani ba.

Kotun ta ce matakin da Gwamna Fubara ya ɗauka na gabatar da kasafin kuɗin ga mambobin majalisar guda huɗu daga cikin 31, ya saɓawa sashe na 91 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 wanda aka yi kwaskwarima.

Kara karanta wannan

'Yancin kananan hukumomi: Majalisa ta cimma matsaya, ta gargadi gwamnoni

Wike ya ba Gwamna Fubara shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, shawara kan rikicin da yake faruwa a jihar.

Nyesom Wike ya buƙaci magajin nasa da ya riƙa bin doka da oda domin a samun zaman lafiya a jihar da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng