Farashin Fetur: Atiku Ya Yi wa Tinubu Sabon Lakabi, Ya Zarge Shi da Kuntata wa Jama'a

Farashin Fetur: Atiku Ya Yi wa Tinubu Sabon Lakabi, Ya Zarge Shi da Kuntata wa Jama'a

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi Bola Tinubu da watsi da jama'a duk da kuncin da ake ciki
  • Atiku na wannan batu ne biyo bayan karin farashin litar fetur da kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya yi zuwa sama da N1,000
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar ya caccaki Tinubu, ya ce ba ya damuwa da halin da gwamnatinsa ta jefa jama'a a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya sa wa shugaban kasa Bola Tinubu lakabin 'TPain' bayan an samu karin farashin fetur.

Kara karanta wannan

Bayan sayen fetur da sauki, yan kasuwa sun zargi NNPCL da tsuga masu farashi

Yan Najeriya sun fusata bayan kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya kara farashin litar fetur da ya ke sayar masu a fadin kasar nan.

Atiku
Atiku ya caccaki Tinubu kan tsadar fetur Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya zargi shugaban kasar da biris da halin da jama'ar kasar nan ke ciki biyo bayan karin farashin fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya soki karin farashin fetur

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa kare-karen farashin fetur babu tsari ne ya jefa mutane cikin wahala.

Atiku Abubakar ya kara da cewa tun da fari, yadda gwamnatin Bola Tinubu ta dauko maganar tallafin man fetur aka fara samun matsalar tattalin arziki.

"Tinubu bai damu da talaka ba" - Atiku

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da bangaren fetur ya jefa jama'a cikin wahala.

Kara karanta wannan

"A kashe mu a huta:" Yan Najeriya sun koka da karin farashin litar man fetur

Amma ya yi takaicin yadda a ganinsa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke nuna halin ko in kula da wahalhalun da jama'a ke fuskanta.

Atiku ya soki gwamnatin Tinubu

A baya mun wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya caccaki yadda gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da mulki.

Atiku ya zargi gwamnatin da take hakkin dan Adam da na kungiyoyi masu fafutukar tabbatar da adalci da kwato hakkin yan Najeriya da ya yi zargin gwamnati na murkushewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.