Bayan Kara Kudin Fetur, PETROAN Ta Fadawa Dangote Matakin da Ya Kamata Ya Dauka

Bayan Kara Kudin Fetur, PETROAN Ta Fadawa Dangote Matakin da Ya Kamata Ya Dauka

  • Kungiyar masu gidajen mai (PETROAN) ta ba Alhaji Aliko Dangote shawarar abin da ya dace ya yi game da farashin da yake sayar da fetur
  • Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harris, ya ce lokaci ya yi da ya kamata Dangote ya fadawa 'yan kasuwa farashin da yake sayar da man
  • Billy Gillis-Harris ya koka kan yadda har yanzu kamfanin NNPCL ne kadai ke iya magana kai tsaye da Dangote kan cinikayyar man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar masu gidajen mai (PETROAN), ta bayyana takaici kan yadda matatar Dangote ke ci gaba da kin bayyana hakikanin farashin da take sayar da fetur.

PETROAN ta yi magana ne awanni bayan da rahotanni suka nuna cewa kamfanin NNPCL ya kara kudin fetur zuwa N1,030 kan kowacce lita daya.

Kara karanta wannan

Bayan sayen fetur da sauki, yan kasuwa sun zargi NNPCL da tsuga masu farashi

PETROAN ta yi magana kan shirun da Dangote ya yi game da farashin man fetur.
Kungiyar PETROAN ta bukaci Dangote ya fadawa 'yan kasuwa farashin mansa. Hoto: Bloomberg / Contributor
Asali: Getty Images

Matatar Dangote ba ta kawo sauki ba

Da yake magana a shirin safe na Channels TV, a ranar Alhamis, shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harris ya ce lokaci ya yi da Dangote zai rika magana kai tsaye da dillalan mai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kyautata zaton fara sayar da man fetur da matatar Dangote ta yi zai rage tashin farashin fetur din a Najeriya, sai dai har yanzu akasin hakan ake gani.

Matatar ta kyale kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya zama 'dan tsakiya', inda yake saye a wurinsu tare da sayar wa 'yan kasuwa.

Billy Gillis-Harris ya nuna cewa yanzu lokaci ne da Dangote zai cire 'dan tsakiya' a alakarsa da 'yan kasuwa da kuma masu ruwa da tsaki.

PETROAN ta aika sako ga Dangote

Shugaban kungiyar ta PETROAN ya ce:

"A wannan lokacin lamura ke canjawa a Najeriya, ya kamata masu gidajen mai irinmu su san nawa Dangote yake son siyar mana da man fetur.

Kara karanta wannan

Karin farashin fetur: NLC ta dauki zafi kan lamarin, ta ja kunnen Tinubu da NNPCL

“NNPC ta ba mu samfurin farashi, wanda bai bayyana mana ainihin farashin da Dangote ya sayar da man ba. Ya kamata Dangote ya fara magana kai tsaye da 'yan kasuwa."

Duk da cewa kamfani ne mai zaman kansa, Gillis-Harris ya ce akwai bukatar Dangote ya fito fili ya rika yi wa masu gidajen mai, 'yan kasuwa da masu ruwa da tsaki bayani kan farashin man.

NNPCL ya sake kara kudin fetur

Tun da fari, mun ruwaito cewa gidajen man NNPCPL a Legas sun kara farashin fetur daga N855 zuwa N998 yayin da a Abuja NNPCL ya kara kudin litar zuwa N1,030 daga N897.

A jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, an ce za a rika sayar da litar man fetur a kan N1,070 yayin da ya kai N1,030 a Arewa ta Tsakiya da N1,075 a Arewa maso Gabas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.