An Kama Manyan Yan Bindiga da Suka Fitini Jihohin Arewa Tsawon Shekaru

An Kama Manyan Yan Bindiga da Suka Fitini Jihohin Arewa Tsawon Shekaru

  • Rundunar sojin Najeriya ta samu nasara kan yan ta'adda masu garkuwa da mutane a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
  • An kama manyan yan ta'adda uku da ake zargin sun dauki shekaru suna mummunan ta'addanci tsakanin jihohin Taraba da Filato
  • Haka zalika rundunar sojin ta cafke wani mutum a garin Lau da ake zargin yana cikin masu samar da makamai ga miyagun yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu yan ta'adda da suka dauki shekaru suna ta'addanci.

Rahotanni sun nuna cewa an kama miyagun ne a wani yanki da ya haɗa iyaka tsakanin Taraba da Filato.

Kara karanta wannan

Sojoji sun mayar da martani ga Dokubo Asari kan barazanar kado jirginsu daga sama

sojoji
Sojoji sun kama yan bindiga a Taraba. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa rundunar sojin ta cafke wani mutum mai suna Musa Inusa da ake zargi da safarar makamai ga yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama manyan yan bindiga a Taraba

Sojojin Najeriya sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da fitinan al'umma da sace mutane a yankunan Taraba da Filato.

Hakan ya biyo bayan wani samame na musamman da rundunar sojin ta yi ne a ranar 7 ga watan Oktoba a karamar hukumar Karim Lamido.

Ta'addanci da yan bindigar suke yi

Ana zargin mutanen ne da yin fashi da makami, garkuwa da mutane da kai munanan hare hare kan ƙauyuka.

Binciken soji ya tabbatar da cewa yan bindigar sun yi shekaru suna ta'addanci a yankunan jihohin ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

An kama mai taimakon yan bindiga

Kara karanta wannan

Farashin fetur: Ministar Tinubu ta yi albishir mai daɗi ga yan Najeriya

A wani farmaki da sojoji suka kai a karamar hukumar Lau sun cafke wani mutum da ake zargi da safarar makamai da wasu kayayyaki ga yan bindiga.

Daily Post ta wallafa cewa wanda ake zargin, Musa Inusa yana da alaka da muggan yan bindiga a jihar Taraba.

An kama sarki kan taimakon yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Katsina ta cafke wani basarake da ake zargi da taimakon yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun kama basaraken ne a wani yankin jihar Kaduna bayan samun bayanan sirri a kansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng