Hankali Ya Tashi yayin da Wata Mata da Jikokinta 4 Suka Bakunci Lahira daga Shan Koko

Hankali Ya Tashi yayin da Wata Mata da Jikokinta 4 Suka Bakunci Lahira daga Shan Koko

  • An shiga tashin hankali a unguwar Gaga da ke Oke Aro a Akure yayin da wata mata da jikokinta hudu suka bakunci lahira daga shan koko
  • An ce dattijuwar ce ta fara mutuwa bayan shan kokon, sai danginta suka dauki mutuwarta a matsayin cikar wa'adi ba tare da zargin komai ba
  • Sai dai bayan jikokin matar su ma sun sun sha kokon, sun kamu da bacin ciki, inda aka garzaya da su asibiti amma suka mutu bayan awanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Ana fargabar bacin ciki daga cin lalataccen abinci ya kashe mutane da suka hada da wata dattijuwa da jikokinta hudu a karamar hukumar Akure ta jihar Ondo.

Kara karanta wannan

"A kashe mu a huta:" Yan Najeriya sun koka da karin farashin litar man fetur

Dattijuwar da jikokinta hudu da ke zaune a titin Atayese, a unguwar Gaga da ke Oke Aro a Akure, sun bakunci lahira ne bayan sun sha koko.

Dattijuwa da jikokinta hudu sun mutu bayan shan koko a Ondo
An shiga tashin hankali bayan dattijuwa da jikokinta 4 sun mutu bayan shan koko.
Asali: Original

Ko da yake lamarin ya faru ne a makon da ya gabata, amma jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya jefa ’yan uwa da makota cikin tashin hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattijuwar ce ta fara mutuwa

Wata majiya mai tushe da ta yi magana a ranar Talata kan lamarin, ta ce tsohuwar ta mutu ne bayan shan kokon kuma na kai gawarta dakin ajiyar gawarwaki.

Majiyar ta ce dangin dattijuwar ba su yi zargin wani abin ne ya kashe ta ba, sun dauki mutuwarta matsayin cikar wa'adi musamman ganin tsufa ya cimmata.

"Bayan mutuwar kakarta, kanwarta da mijinta tare da 'ya'yansu hudu suka je gidanta domin yi kaye kaye, a nan ne suka ga garin koko, wanda 'ya'yan suka bukaci a dama masu."

Kara karanta wannan

Sauye sauye a majalisar ministoci: Tinubu zai saki sunayen ministocin da zai kora

- A cewar majiyar.

Jikoki 4 sun mutu daga shan koko

Majiyar ta ci gaba da cewa:

“Mahaifiyarsu wadda ‘yar uwata ce ta dama masu kokon ta ba ‘ya’yanta da wani dan uwansu da suka je gidan tare. Yaran na da shekaru uku, biyar, bakwai, sai dan uwansu mai 10."

Majiyar ta ce yaran sun fara fuskantar bacin ciki jim kadan da shan kokon, kuma sun mutu kwanaki uku bayan da aka kai su asibiti.

Bacin ciki: 'Yan gida daya sun mutu

A wani labarin, mun ruwaito cewa an shiga jimami bayan wasu 'yan gida daya sun mutu bayan cin abinci da aka yi da miyar gishirin lalle a kauyen Kaurar Wanke, jihar Sokoto.

Binciken da aka yi ya tabbatar da cewa mutane uku ne yan gida daya suka mutu bayan sun sha miyar da aka hada ta da gishirin lalle bisa kuskure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.