Sojoji Sun Mayar da Martani ga Dokubo Asari kan Barazanar Kado Jirginsu daga Sama

Sojoji Sun Mayar da Martani ga Dokubo Asari kan Barazanar Kado Jirginsu daga Sama

  • Rundunar sojoji a Najeriya ta mayar da martani ga dan gwagwarmaya, Asari Dokubo kan barazanar kado jirginsu
  • Rundunar ta ce Dokubo ba shi da jarumta ko wata kwarewa da kayan aiki da zai iya kai hari kan jiragun sojoji a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan ya yi barazana ga sojoji kan kifar da jiragensu da ke shawagi a saman gidansa da ke Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar tsaro ta yi magana kan barazanar kifar da jirgin sama da Asari Dokubo ya yi mata.

Rundunar ta ce Dokubo ba shi da kayan aiki ko jarumtar da zai iya kifar da jirgin sojoji kan zargin shawagi a saman gidansa yayin rikcin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

'Ya mutu har lahira,' Sojoji sun yi rubdugu ga dan sanda, sun lakaɗa masa duka

Sojoji sun gargadi Dokubo kan barazanar kifar da jirginsu daga sama
Rundunar sojoji sun mayar da martani ga Asari Dokubo. Hoto: Dakubo-Asari, HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Dokubo ya yi barazana ga jirgin sojoji

Daraktan yada labaran rundunar, Manjo-janar Edward Buba shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin na zuwa ne bayan Dokubo ya fito a wani faifan bidiyo inda yake gargadin sojoji kan shawagi da suke yi a saman gidansa.

Hakan ya biyo bayan rikicin Rivers tsakanin tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara.

Rigimar ta jawo rasa rayuka da kona dukiyoyi yayin gudanar da zaben kananan hukumomo da aka yi cikin fargaba.

Rundunar tsaro ta yiwa Dokubo martani

Cikin martaninsa, Edward Buba ya ce Dokubo surutu yake yi kawai babu abin da zai iya yi kan barazanar da ya yi.

Buba ya ce hukumomin tsaro da dama na amfani da jiragen sama wurin samar da tsaro ga yan kasa cikin kwarewa a karkashin tsarin dimukradiyya.

Kara karanta wannan

Shinkafa: An tsare Janar kan handame tallafin Tinubu a Kano, za a iya yi masa ritaya

An bukaci cafke Asari Dokubo kan barazana

Kun ji cewa ana ta kiraye-kiraye ga Gwamnatin Tarayya ta kama tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Alhaji Asari Dokubo.

A farkon watan Yuni, an gano Dokubo a cikin wani bidiyo da ya yadu rike da bindigar AK-47 yana barazanar shafe inyamurai.

A bidiyon, ya yi masu ba'a, yana mai cewa ba don Turawa da suka shigo lamarin ba da har yanzu yana nan yana siyar da su a matsayin bayi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.