Duk Lita N630: Kwastam Ta Karya Farashin Fetur, Ta Ware Gidajen Mai

Duk Lita N630: Kwastam Ta Karya Farashin Fetur, Ta Ware Gidajen Mai

  • Hukumar kwastam ta kaddamar da fara sayar da man fetur a kan farashi mai rahusa a wasu gidajen mai da ta ware
  • Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi ya ce hakan na cikin kokarin da suke yi domin kawo saukin rayuwa
  • A ranar Laraba ne aka wayi gari da karin kudin man fetur a fadin Najeriya inda litar mai ta haura N1,000 a mafi yawan jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - Hukumar kwastam ta karya farashin man fetur domin kawo saukin rayuwa ga al'ummar Adamawa.

Rahotanni sun nuna cewa hukumar kwastam ta ware wasu gidajen mai da za ta rika sayar da mai a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Bayan sayen fetur da sauki, yan kasuwa sun zargi NNPCL da tsuga masu farashi

Kwastam
Kwastam ta karya farashin man fetur a Adamawa. Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa man fetur din da za a sayar yana da yawa sosai kudinsa ya haura Naira miliyan 155.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwastam ta karya farashin man fetur

Hukumar kwastam ta karya farashin man fetur a jihar Adamawa inda za ta rika sayar da lita a kan N630.

Tribune ta ruwaito cewa an kaddamar da sayar da man fetur mai saukin kudin ne a wasu gidajen mai guda biyu a fadin jihar.

A yanzu haka dai farashin litar man fetur a gidajen man kamfanin NNPCL a jihar Adamawa ya haura N1,000.

A ina kwastam ta samo fetur mai sauki?

Hukumar kwastam ta bayyana cewa ta kwace fetur kimanin lita 94,550 a wajen masu shirin fita da shi kasashen waje ta barauniyar hanya.

Hakan na nuni da cewa hukumar kwastam za ta sayar da man da ta kwace ne kuma idan ya kare shi kenan kasuwar za ta tsaya.

Kara karanta wannan

Sabon farashin mai: Jerin jihohin da fetur ya fi araha da inda ya fi tsada

Kwastam ta bayyana cewa dukkan al'umma suna da yancin zuwa gidajen man da aka ware domin sayen fetur a farashin da ta karya.

NLC ta koka kan karin kudin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Kwadago ta NLC ta yi Allah wadai da karin farashin man fetur da NNPCL ya yi a fadin Najeriya.

Kungiyar kwadago ta caccaki kamfanin NNPCL, ta ce bai kamata ya ke yanke farashi ba a matsayinsa na kamfani mai zaman kansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng