Badakalar N33bn: Yadda Tsohon Ministan Buhari Ya Siya Kadarori da Kudin Kwangila

Badakalar N33bn: Yadda Tsohon Ministan Buhari Ya Siya Kadarori da Kudin Kwangila

  • Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gabatar da shaida a ƙarar da ta shigar kan tsohon minista, Saleh Mamman
  • Shaidan na EFCC ya gayawa kotu tsohon ministan ya yi amfani da kuɗin aikin lantarki na Mambilla wajen siyan kadarori a Abuja
  • Ministan na gwamnatin Muhammadu Buhari yana fuskantar tuhume-tuhume ne kan zargin karkatar da N33.8bn lokacin yana ofis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An ci gaba da shari'ar tsohon ministan makamashi a gwamnatin Muhammadu Buhari, Saleh Mamman.

Wani jami'in hukumar EFCC, Abubakar Kweido ya gayawa kotu cewa tsohon ministan ya yi amfani da kuɗin aikin samar da lantarki a Mambilla wajen wajen siyan kadarori a unguwar Wuse da Kado a Abuja.

Kara karanta wannan

Buhari ya tura tsofaffin Ministocinsa 10 yin ta'azziya, ya ba iyalan ministarsa shawara

EFCC ta kawo shaida kan Saleh Mamman
Shaidan EFCC ya ba da bayanai kan tuhumar da ake yi wa Saleh Mamman Hoto: Economic and Financial Crimes Commission, Saleh Mamman
Asali: Facebook

Abubakar Kweido shi ne shaida na farko da hukumar EFCC ta gabatar a tuhumar da take yi wa Saleh Mamman kan zargin karkatar da N33.8bn, cewar rahoton jaridar PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Saleh Mamman ya siya kadarori

A yayin zaman kotu na ranar Laraba, Abubakar Kweido, ya ce bincike ya nuna cewa an yi amfani da wasu kuɗin da aka sakarwa tsohon ministan wajen siyan kadarori a Kado Estate da Wuse 2 a birnin tarayya Abuja.

"Mun gayyaci ministan sannan muka nuna masa abin da binciken mu ya nuna a gaban lauyansa. Ya musanta cewa yana da alaƙa da kadarorin."
"Mun gudanar da bincike a gidan ministan inda muka ƙwato wasu kuɗin ƙasashen waje."
"Mun kuma ƙwato takardun shaidar rajista da CAC na kamfanin Abangus Nig. Ltd wanda bincike ya nuna cewa yana ɗaya daga cikin abin da ministan yake amfani da shi wajen karkatar da kuɗi daga asusun aikin Mambilla."

Kara karanta wannan

"Ba Buhari ba ne": An bayyana wanda ya yi gaban kansa wajen sauya fasalin Naira

- Abubakar Kweido

Hujjojin da hukumar EFCC ta samu

An shigar da takardun shaidan biyan kuɗi na kamfanin Abangus Nig. Ltd da fom ɗin kuɗin da aka ƙwato a gidan tsohon ministan a matsayin shaida.

Alƙalin kotun James Omotosho ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar, 23 ga watan Oktoban 2024.

EFCC ta cafke Saleh Mamman

A wani labarin kuma, kun ji cewa EFCC ta cafke tsohon ministan makamashi a gwamnatin Buhari, Saleh Mamman kan tuhumar shi da badaƙalar N22bn.

Kamen yana da alaƙa da wani bincike da hukumar ta ke gudanarwa kan badaƙalar da aka yi wajen ƙaddamar da wasu ayyukan wutar lantarki a lokacin da yake matsayin minista.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng