Matasa Sun Ba Shi Guba, Sun Caccakawa Mai gidansu Wuƙa, Sun Ƙona Gawarsa Ƙurmus
- Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke wasu matasa uku bisa zargin kashe wani magidanci da banka wuta ga gawarsa
- Kakakin rundunar yan sandan Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa ya sanar da yadda matasan suka kashe mutumin, suka kona shi
- Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya yi kira ga al'umma kan yin taka tsantsan da mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta cafke wasu matasa uku bisa zargin kisan kai tare da kona gawa.
Bayanan yan sanda sun nuna cewa matasan sun ba mutumin da suka kashe guba ne kafin sun karasa kashe shi.
Kakakin yan sandan jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa ne ya wallafa bidiyon yadda abin ya faru a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa sun kashe mai gidansu a Kano
Ana zargin wasu matasa su uku da kashe wani magidanci mai suna Dahiru Musa domin mallakar filinsa.
Daya daga cikin matasan ya gayyaci Dahiru Musa gidansa inda suka sanya masa guba a cikin abinci.
Bayan sanya masa guba a abinci ya fara tari amma da suka ga bai mutu ba sai suka nemo wuka suka caccaka masa.
Matasan sun kona gawar mai gidansu
Bayan kashe Dahiru Musa, sai suka rasa yadda za su yi su boye gawarsa, don haka suka nemo fetur suka banka masa wuta.
Jagoran matasan mai suna Aliyu ya bayyana cewa a karon farko sun boye gawar mai gidan nasu ne a wani kango bayan sun kashe shi..
Maganar kwamishinan yan sandan Kano
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya yi kira ga al'umma kan yin taka tsantsan wajen yarda da mutane sosai.
Rundunar yan sanda ta ce za ta mika waɗanda ake zargin gaban kotu domin musu hukuncin da ya kamata.
An kama sarki da taimakon yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Katsina ta cafke wani basarake da ake zargi da taimakon yan bindiga.
Rahotanni sun tabbabar da cewa yan sanda sun kama basaraken ne a yankin jihar Kaduna bayan samun bayanan sirri a kansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng