Gwamnatin Tinubu Ta Jajubo Rancen $6.45bn daga Bankin Duniya a Watanni 16

Gwamnatin Tinubu Ta Jajubo Rancen $6.45bn daga Bankin Duniya a Watanni 16

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta laftowa kasar nan bashin Bankin Duniya a 'yan watannin da shugaban ya kama aiki
  • Rahotanni sun bayyana cewa a cikin watanni 16 kawai, gwamnatin tarayya ta karbo Dala biliyan 6.45 daga Bankin Duniya
  • Wannan na nufin bashin da babban bankin ke bin kasar nan ya yi tsalle zuwa Dala biliyan $24.088 a cikin shekaru biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta karbo rancen makudan Daloli daga Bankin Duniya a cikin watanni 16 da shugaban ya fara mulkin kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

Rahotanni sun tabbatar da cewa a dan tsakanin wannan lokaci, gwamnatin Najeriya ta karbi rancen $6.45bn daga Bankin Duniya.

Tinubu
Najeriya ta ranto $6.45bn daga bankin duniya a watanni 16 Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa rancen da kasar nan ke karbowa ya karu ne bayan bankin ya amince da ba gwamnatin Tinubu karin rancen $1.57bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin Duniya na kara tilawa Najeriya bashi

Bankin Duniya na kara ba kasar nan rancen kudade, inda aka tabbatar da cewa bankin ya ba wa Najeriya rance sau 36 a cikin shekaru biyar.

Jimlatan, bashin da bankin ke bin kasar nan ya kai $24.088bn a wannan shekaru da ake sa ran za a yi amfani da kudin wajen aiwatar da ayyukan raya kasa.

Bashin da bankin duniya ya ba Najeriya

Daga cikin basussukan da gwamnatin Bola Tinubu ta karba akwai $750m na aikin gyaran bangaren lantarki, da $500m na tallafawa mata a kasar.

Kara karanta wannan

Masanin tattalin arziki ya fadi dabarar da za ta karya farashin kayan abinci farat daya

Sauran sun hada da $700m domin farfado da ilimin yara mata da $1.5m na daidaita tattalin arzikin kasa sai $750m na samar da makamashin mara gurbata yanayi.

Bankin duniya: Najeriya ta ranto $2.25bn

A wani labarin, kun ji cewa duk da kuka da masana ke yi na tilin bashin da Najeriya ke karbowa daga wurare daban daban, gwamnatin Bola Tinubu ta sake aro kudi.

Rahotanni sun bayyana cewa an karbo rancen $2.25bn daga Bankin Duniya a watan Yunin 2024 kuma ana sa ran gudanar da manyan ayyuka guda biyu da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.