'Ka Biya Mu daga Tushe', Sarakuna a Arewa Sun Roki Tinubu kan Biyansu Hakkokinsu
- Wasu sarakunan gargajiya a Najeriya sun nuna damuwa kan yadda ake samun matsala game da kudin da ake ware musu
- Sarakuna daga jihar Nassarawa sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta rika ba su kasonsu na 5% daga tushe domin yin adalci
- Wannan na zuwa ne bayan korafi kan yadda ake hada musu kason nasu a kudin ƙananan hukumomi wanda ake samun matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Sarakunan gargajiya a Najeriya sun roki Gwamnatin Tarayya alfarma kan kason kudi da ake ba su.
Sarakunan sun bukaci biyansu kudi 5% da aka ware musu na musamman a rika biyansu daga tushe.
Sarakuna sun roki Tinubu kan hakkokinsu
Leadership ta ce daman ana haɗawa sarakunan ne a cikin kudin kananan hukumomi domin ba su kasonsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chun Mada na Akwanga, Dakta Samson Gamu shi ya roki Gwamnatin Tarayya a madadin sauran sarakunan gargajiya a jihar Nasarawa.
Basaraken ya bayyana haka yayin da suka kai wa shugaban Hukumar tattarawa da raba kudi a Najeriya, RMAFC, Mohamed Bello Shehu a Abuja.
Sarakunan sun yabawa shugaba Bola Tinubu kan yadda ya himmatu wurin tabbatar da yancin kananan hukumomi, The Nation ta ruwaito.
"Duk da samun cigaba da aka yi kan 5% na sarakunan gargajiya, ana fuskantar matsala wurin isowar kudin inda ya dace."
"Ba mu amince da yadda ake cire kudin ba domin babu adalci da bayyana komai a fili."
- Sarakunan gargajiya
Gwamnatin Tarayya ta yabawa sarakunan gargajiya
Shugaban hukumar RMAFC, Mohamed Bello Shehu ya bayyana muhimmancin sarakunan gargajiya a cikin al'umma.
Bello Shehu ya ce sarakunan ba iya bangaren al'adu suke taka rawa ba har ma da kasancewa jagororin kawo cigaba a kasa.
Gwamnoni na kokarin dakile yancin kananan hukumomi
Kun ji cewa Majalisar dattawa ta yi wata ganawa ta musamman a Abuja kan abin da ya shafi samun yancin kananan hukumomi a Najeriya.
Majalisar ta zargi wasu gwamnoni da hada baki da Majalisun jihohinsu domin kwace kudin kananan hukumomi daga Gwamnatin Tarayya.
Wannan na zuwa ne yayin da wasu gwamnoni ke kokarin kakaba wata doka a jihohinsu domin karkatar da kudin kananan hukumomi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng