Boko Haram: Sanata Ndume Ya Fadi Gaskiya kan Kai Masa Hari

Boko Haram: Sanata Ndume Ya Fadi Gaskiya kan Kai Masa Hari

  • Muhammadu Ali Ndume ya yi magana bayan labari ya bazu cewa an kai masa hari a hanyarsa ta dawowa daga ta’aziyya
  • Ndume ya ce akwai matsalolin da su ke hana dakarun sojojin kasar nan da sauran jami’an tsaro magance matsalar ta’addancin
  • Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattijai ya yi magana bayan 'yan Boko Haram sun shiga Gwoza sun yi ta'adi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Sanata Ali Ndume ya bayyana ainihin abin da ya faru kan labarin da ake yadawa na cewa yan kungiyar Boko Haram sun kai masa hari.

Sanatan, wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji ya kuma fadi abubuwan da su ka hana dakarun sojojin kasar nan samun nasara kan yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

Ali Ndume
Sanata Ndume ya musanta cewa Boko Haram sun kai masa hari Hoto: Sen. Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an rika yada labari wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun yi wa tawagar motocin Sanatan kwantan bauna a Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ndume ya musanta kai masa hari

Jaridar Daily Post ta tattaro cewa Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu da Gwoza, Ali Ndume ya karyata labarin cewa yan Boko Haram sun kai masa hari.

Ya musanta labarin harin ne a Maiduguri jim kadan bayan dawowarsa daga ta’aziyyar wadanda yan ta’addan Boko Haram su ka kashe a kauyukan Ngoshe, Kirawa, Ashigashiya da wasu wuraren a karamar hukumar Gwoza.

“A hanyarmu ta zuwa ta’aziyya aka kira mu, aka sanar da mu cewa an yi wa wasu sojojin Kamaru da matafiya kwantan bauna a hanyar Pulka-Kirawa.”

Sanata Ndume ya gano matsalar yakin ta'addanci

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa rashin isassun kayan aiki na zamani na daga cikin dalilan da ya ke kawo nakasu a kan yaki da ta’addanci a kasar nan.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Dattawan Arewa za su nemo hanyar magance matsalar tsaro

Ya kara da cewa haka kuma jami’an sojojin kasar nan ba sa samun goyon baya da karfafa gwiwar aiki yadda ya dace.

Sanatan Borno ya bayar da shawarar samun tsaro

A baya kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan daukar wasu matakai da ya ke ganin za su kakkabe ta’addanci.

Sanata Ndume ya ce kamata ya yi a dauko sojojin haya daga kasashen ketare, domin su na da kwarewa da manyan makaman da ake bukata wajen maganin yan ta’adda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.