"Babu Ruwanmu": Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Yin Karin Farashin Man Fetur

"Babu Ruwanmu": Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Yin Karin Farashin Man Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta fito ta yi magana kan tashin gwauron zabi da farashin man fetur ya yi a ƙasar nan a jiya Laraba
  • Ministan yaɗa labarai ya bayyana cewa ba gwamnatin tarayya ba ce ke da alhaki kan ƙarin farashin da NNPCL ya yi
  • Mohammed Idris ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri domin nan ba da jimawa farashin man fetur zai sauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba ita ba ce ta yi ƙarin farashin kuɗin man fetur.

A ranar Laraba ne dai kamfanin NNPCL ya ƙara farashin man fetur zuwa N1,030 a Abuja, N998 a Legas, N1, 070 a Arewa maso Gabas, N1,025 a wasu jihohin Kudu-maso-Yamma, N1,045 a Kudu maso Gabas da kuma N1,075 a Kudu maso Kudu. 

Kara karanta wannan

"Ba dai N1,000 ba kuma": Farashin litar man fetur ya sake tashi a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan karin farashin fetur
Gwamnati ta ce ba ita ta yi karin farashin fetur ba Hoto: @FMINONigeria
Asali: Twitter

Gwamnati ta kara kudin man fetur?

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ya yi bayani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Idris ya ce ba gwamnatin tarayya ba ce ke da alhaki kan ƙara kuɗin man fetur ɗin.

Meyasa NNPCL ya ƙara farashin fetur?

Ministan ya bayyana cewa NNPCL ya yanke wannan shawarar ƙarin farashin fetur ne saboda abubuwan da ke faruwa a ɓangaren makamashi.

Ministan ya jaddada cewa ba gwamnati ba ce ta ba kamfanin umarnin yin ƙarin domin yanzu ta daina ƙayyade farashin man fetur kamar yadda aka tanada a dokar masana'antar man fetur (PIA).

Mohammed Idris ya ce tun da tsarin biyan tallafin mai ya ƙare a watan Mayun 2023, NNPCL yana biyan wani kaso ne domin ka da farashin ya tashi sosai, amma yanzu ba zai iya hakan ba saboda asarar da yake yi.

Kara karanta wannan

N77,000: NYSC ta fadi dalilin kasa fara biyan sabon alawus

Ministan ya bukaci ƴan Najeriya da su ci gaba da nuna fahimta ga kamfanin NNPCL da gwamnati, inda ya tabbatar da cewa nan gaba kaɗan farashin zai sauka.

NLC ta soki ƙarin farashin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta yi magana kan ƙarin kudin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi a ƙasar nan.

Kungiyar ta yi Allah wadai da matakin kara farashin daga N897 zuwa N1,030 a wasu wurare, ta buƙaci gwamnatin tarayya ta yi gaggawar janye karin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng