'Ba Ku Ci Wuya ba', Ministan Buhari Ya Soki Yadda Matasa Suka Yi Sanyi a Zanga Zanga

'Ba Ku Ci Wuya ba', Ministan Buhari Ya Soki Yadda Matasa Suka Yi Sanyi a Zanga Zanga

  • Tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan halin aka jefa yan Najeriya a ciki a yanzu
  • Rotimi Amaechi ya ce kwata-kwata yan Najeriya sun yi sakaci musamman lokacin da aka gudanar da zanga-zanga
  • Ya ce ya yi tsammanin bacin ran mutane musamman matasa zai zarce yadda ya gani yayin zanga-zangar da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi ya yi magana kan halin kunci da ake ciki.

Rotimi Amaechi ya ce bai ji dadin yadda yan Najeriya suka yi gum da bakinsu duk da halin da suke ciki ba.

Kara karanta wannan

Manyan yan siyasa a Arewa da aka zarge su da hannu a ayyukan ta'addanci

Ministan Buhari ya soki matasa kan rashin nuna fushinsu kan halin kunci
Tsohon Minista, Rotimi Amaechi ya ce ya yi tsammanin bacin rai sosai daga matasa kan halin kunci. Hoto: Hon. Rotimi Amaechi.
Asali: Facebook

Halin kunci: Amaechi ya soki matasan Najeriya

Tsohon gwamnan Rivers ya bayyana haka yayin wata hira da dan jarida wanda Punch ta bibiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaechi ya ce ya yi tsammanin yan Najeriya za su nuna fushinsu yayin zanga-zanga fiye da abin da suka yi.

Tsohon Ministan ya ce ya yi tsammanin fiye da haka daga matasa musamman duba da mummunan yanayi da aka shiga a kasar.

Abin da Amaechi ya yi tsammani daga matasan

"Na yi tsammanin ganin bacin ran yan kasa musamman matasa saboda halin da aka shiga na tsadar rayuwa."
"Ina tsammani ganin fiye da haka a kan tituna saboda mutane ba su nuna bacin ransu kamar yadda na yi tsammani ba."

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya ce babu wani hobbasa daga yan Najeriya kan halin da suke ciki domin tunkarar gwamnati, cewar rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Mutane 4 da za su iya kawo karshen rikicin siyasar jihar Ribas

NLC ta gargadi Tinubu kan kara farashin mai

Mun baku labarin cewa Kungiyar Kwadago ta NLC ta nuna damuwa kan yadda kamfanin NNPCL ya kara kudin mai a yau Laraba 9 ga watan Oktoban 2024.

Kungiyar ta yi Allah wadai da matakin inda ta bukaci Bola Tinubu ya yi gaggawar mayar da tsohon farashi inda ta ce ana kara talauta al'umma a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan karin kudin mai daga N897 zuwa N1,070 a gidajen mai na kamfanin NNPCL a wurare da dama da ke fadin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.