Gwamnan APC Ya Yi Biris da Korafin Al'umma, Ya Sake Ware N95.4m na Gyaran Masallatai

Gwamnan APC Ya Yi Biris da Korafin Al'umma, Ya Sake Ware N95.4m na Gyaran Masallatai

  • Duk da korafe-korafe kan Gwamna Ahmed Aliyu na ware makudan kudi kan ayyuka, gwamnatin Sokoto za ta ba masallatai N95.4m
  • Mai girma Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya ware kudin ne domin gyara masallatan Juma'a guda 87 a jihar saboda inganta su
  • Wannan na zuwa ne bayan shan suka fa gwamnan ke yi wurin ware biliyoyi a wasu ayyuka da ake ganin ba su cancanci kudin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta sake ware makudan kudi domin gyaran masallatan Juma'a.

Gwamna Ahmed Aliyu ya ware akalla N95.4m domin gyara masallatan Juma'a da ke fadin jihar guda 87.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rugurguza katafaren ginin babba a APC cikin dare, an fara cacar baki

Gwamnan APC zai gyara masallatan Juma'a da kudi N95.4m
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto zai gyara masallatan Juma'a kan kudi N95.4m. Hoto: Ahmed Aliyu.
Asali: Facebook

Yadda aka kasafta masallatan Sokoto gida 3

Da ya ke mika kudin a yau Laraba 9 ga watan Oktoban 2024, Daily Trust ta ce gwamnan ya tabbatar da cewa za a rarraba masallatan gida uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Aliyu ya ce masallatai 20 za su samu N500,000 daga kudin sai kuma guda 17 su karbi N400,000.

Gwamnan Sokoto ya ce kowane masallaci daga cikin guda 50 kuma zai samu makudan kudi har N300,000.

Har ila yau, gwamnan ya ce an ware kudin ne na watanni uku da suka hada da Agusta da Satumba da kuma Oktoban 2024.

Gwamnan ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bello Goronyo wanda ya hakan na daga cikin himmatuwar gwamnatin wurin inganta harkokin addini.

Sultan ya yabawa Gwamna Aliyu na Sokoto

A martaninsa, Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya yabawa gwamnan, ya ce wannan abin koyi ne ga sauran jihohi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya fadi babban burin da ya ke son cimmawa a zaben 2027

Ya shawarci kwamitcocin masallatan da su tabbatar an yi amfani da kudin yadda ya dace ba tare da matsala ba.

Gwamna ya caccaki PDP kan kwangilar N30bn

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Sakkwato ta zargi jam'iyyar adawa ta PDP da yada karya kan ayyukan da ta ke yi wa jama'a.

Gwamna Ahmed Aliyu ya zargi PDP da daukar nauyin yada labaran karya kan kwangilar shingen titunan jihar da aka ware.

Martanin na zuwa bayan PDP ta nemi hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta bincike gwamnatin Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.